Ilimi kogi ne:Na Shaikh Dakta Yusuf Ali Tudun Maliki Kano.
Addu'ar kawo arziki
Kuma cewa Manzon Allah ya kwana uku bai shiga dakin Nana Ai'sha ba, ba haka bane. Cewa ya yi da Mala'ika, me ya sa ba ka zuwa? Sai ya ce saboda akwai hoto a cikin gidan. "Mu kuma idan akwai hoto a gida ba ma shiga." Sai Manzon Allah ya shiga, ya ce da ita ta cire shi. Sai ta yanka shi ta yi filo da shi.
Kuma wata rana yana sallah sai hoton yana daukar hankalinsa, sai ya ce, "ki cire hoton nan saboda yana daukar mani hankali." Ka ga wannan ba ya nuna haramun bane shi. Saboda idan yana sallah ne yana dauke masa kankali ne. Saboda haka Malamai wadanda suka tsananta, irin su Shaikh Nasirudden Albani, sun tsaananta a kan hoto kowane iri. To amma Malamai mafiya yawa suka ce, hoto idan ya kasance ba mai inuwa bane (ba komai).Akwai hoto mai inuwa da kuma mara inuwa, wato wanda za a sassaka da dutse ko itace, kamar gumaka, ko dai a aje shi don ado a gona ko gida da sauransu. To irin wadannan sune suka ce haramun ne. Amma wanda ya kasance ba mai inuwa ba, wannan ba haramun bane. Haka nan idan ya zama akwai bukata ko a jikin kudi ne ko Fasfo da I D, to wannan duk ba matsala. Kuma har yanzu idan ya zama na wasan yara ne, kamar 'yar tsana, ko na maza ko mata, shi ma wannan halas ne. Saboda Manzon Allah (SAW) ya zo wajen Nana Ai'sha tana wasan 'yar tsana, ya leka ya ce, wannan menene? Sai ta ce dakin 'yata ne.Ya ce, wancan meye? Sai ta ce dokina ne. Sai ya ce ya nake ganin doki da fuka-fuki? Sai ta ce kai ba ka san dokin Annabi Sulaimana bane? Sai ya yi dariya kawai, bai hana ta ba.
Saboda haka ya halasta a saya wa yara 'yan mata 'yar tsana don su koyi reno. To wannan duk ba a hana ba. Lamarin mai sauki ne, abin da ake gudu shi ne kar ya kasance wannan hoton, daga baya kuma ka zo ka bauta masa. Shi ne kawai manufar. Wadanda suke halastawan suka ce ai dama farkon Musulunci Annabi (SAW) ya hana a riki hoto, saboda sannan mutane sun kasance "karibul Ahadu" ne. Wato ba su dade ba da barin bautar gumaka. Don haka ya ce a bari. Da aka dade kuma sai ya zama ba ya ma kulawa da wasu abubuwan.
Wannan shi ne a takaice, saboda maganganun suna da yawan gaske.Amma akwai "al halal wal haram" na Dakta Yusuf Alkardawi. Ya bi filla-filla yadda abin yake. Ga wanda yake bukata akwai na Turanci da na Larabci, don shi ne kawai na ga ya bi abin filla-filla haka.
TAMBAYA: Ina neman karin bayani ne dangane da Masallacin kudus da kuma neman maganin ciwon kunnen da ake fama da shi.
DAKTA YUSUF ALI: To game da masallacin kudus, yana da muhimmanci a Addinin Musulunci, don shi ne masallaci na uku a daraja. Masallacin Harami na Makka da kuma na Madina, wato na Manzon Allah (SAW), sai kuma na kudus din. Daga cikin darajojin wakannan Masallatan, yin ibada, kamar sallah raka'a daya tana daidai da sallah raka'a dubu dari. Kuma a masallacin Manzon Allah (SAW) sallah raka'a daya tana daidai da raka'a dubu. Sannan a masallacin kudus kuma raka'a dari biyar.
Don haka ne ya sa a da can idan an tafi aikin hajji, dukkan wuraren sai an je su. A je Makkan, a je Madina, a je kudus. To a yanzu ne dai kuma sha'anin sababbin akidojin nan suka zo suka hana wannan. Amma hakan da tsarin yake.
Annabi Sulaimana ne ya gina wannan Masallacin da shekara arba'in bayan jaddada ginin Ka'aba.To saboda haka, haka tsarin yake. Wato tun bayan ginin Annabi Ibrahin.Yana da muhimmanci kwarai da gaske kuma wajibi ga dukkan musulmi abubuwan da suke faruwa a yanzu, wato kowane musulmi ya yi badin ciki kuma ya yi ta yin addu'a Allah (SWA) ya ku~utar da wannan masallaci daga hannun Yahudawa.
Sai kuma ya ce akwai lokacin da muka yi bayani dangane da maganin ciwon kunne, to "lau anzalna hazak {ur 'ani ala jabalin lara'aitahu," muka ce a rika karantawa. Ana iya karantawa kafa uku da safe a kunnen da yake ciwo a tofa. A karanta da yamma a sake tofawa. Ana kuma iya rubuta ta yadda take din nan da irin su "Allahumma rabban nas..," ita ma kafa uku da kuma Falaki da Nasi su ma kafa uku a tofa a cikin man zaitun. Ko a rubuta da za'afaran a wanke da man zaitun ko kuma ma'ul wardi, to sai a rika digawa a kunnen. An ce ko da kurumta ce, to kunnen mutum zai bude.
TAMBAYA: Ni tambayata ba a ~angaren ilimi bane, ina son in san tarihin Malam ne, saboda na karanta a wata jarida ALMIZAN, cewa ko Malam ya zauna tare da Malam Zakzaky ne, ko sun yi karatu tare ne? Ina son in san dangantakar Malam ne da kuma Malam Ibraheem Zakzaky?
DAKTA YUSUF ALI: To da farko dai yana tambaya ne game da sha'anin rayuwata, kuma wannan wani abu ne da aka saba, mutum yakan taso a rayuwarsa ya yi zamani da wane da wane. Su waye malamansa? Su waye almajiransa? Su waye abokan huldarsa? To ya zama lokacin da ina makarantar sakandare tsakanin shekara ta 1971 zuwa 1974, to a wannan tsakanin mun zauna da shi Shaikh Ibraheem Zakzaky. Kuma ba wai zama haka kawai ba, a' a hulda ta addinin Musuluncin nan ta hada mu. Akwai kungiya ta dalibai musulmi ta makaranta (MSS). Saboda haka ni na zama wakili ne a ciki, ina da matsayi na Odita. Shi kuma ina jin yana Shugaba, to haka muka zauna da ni da shi Shaikh Ibrahim Zakzaky da Muhammad Bala. Wannan babban majistare din nan da ke Gidan Murtala, ina jin kuma gidansa na nan a Sharada, ina jin shi ne mai ba da umurni wajen shari'ar laifi a nan Kano. Da kuma Mujibul Rahman, shi ma dai ana jin sunansa, da sauran mutane da dama. Amma shi Muhammad Bala, a lokacin ya gama makarantarsa. Da shi ma ya zauna cikin kungiyar, saboda haka ya zama kamar shi ne Fatron (Uban kungiyar).
To kuma abin da ya kara wanzar da wannan dangantaka shi ne mun yi hoto da kuma kayan makaranta da 'yar farar hula da 'yan taguwoyi farare. To sai ya zama hoton yana nan. Sai wata rana hakan nan, na dauko hoton na gani, har ma ina jin jaridar Al Mizan sun ta~a kar~a sun buga. To wannan shi ne dangantakarmu da Shaikh Ibraheem Zakzaky.
TAMBAYA: Ina neman barar addu'ar nan ne na jalabi, ina da wata 'yar damuwa ce ina neman Allah (SWA) da ya ba ni budi.
DAKTA YUSUF ALI: To ita dai addu'a kala biyu ce, ko dai kana neman Allah ya ba ka, ko kuma Allah ya tsare ka daga wani abin ki ko sharri, to wannan shi ne ake cewa ko dafa'i ko jalabi. To saboda haka idan an ce jalabi, yana nufin kenan wasu abubuwa da za a yi mutum zai sami wani alkhairi duniya da lahira. Saboda haka abin da za a ba shi ya rika karantawa na game da irin wannan akwai dai ayoyi na arziki ko karantawa ko rubutawa. Wadansu hadisai ne tabbatattu na Manzon Allah (SAW) kamar Izawaka, kamar Alamnashraha, kamar Ya ayyuhal Muzammilu da kul a'uzu bi rabbil falak da Yasin.To wadannan na arziki ne. Da kuma wata aya 'Allahumma rabbana anzil alaina ma'idatan minal sama'i' har zuwa 'wa anta khairur razikin' da kuma 'Ya'atiha rizkuha ragadan min kulli makanin' iya nan, da kuma 'Fammin au amsik li gairi hisab' da 'Inna haza la rizku
ina ma lahum min nafad.' To wadannan ayoyi ne na arziki, ko mutum ya zama irin mai rariyar hannu din nan. Ga shi yana samu, amma sai ya rasa inda abin ya nufa, shi kuma ba shashanci yake yi ba.
Don haka ya danganta da irin girman matsalar da mutum yake ciki. In babba ce kowanne kafa 41. In kuma matsakaiciya ce ana rubutawa kafa 21 kowanne. In kuma karama ce, to ana iya rubutawa kafa 11.
Kuma har yanzu akwai abubuwan da muke bayarwa, misali sunayen nan guda shida wadanda ake karantawa a masallacin Juma'a kafin a yi sallah. Lokacin da Liman yake huduba mutum zai iya yin salatin Annabi 100, ya kuma yi kulhuwallahu 100. Bayan an idar da sallah ya karanta wadannan sunayen kafa 80, 'Ya Mubdi'u, Ya Mudi'u, Ya Rahimu, Ya wadudu, Yaf'aluna ma yurid' da Ya Ganiyyu, Ya Hamidu, Ya Mubdi'u, Ya Mudi'u, Ya Rahimu, Ya Wadudu, Agnini bi halalika an haramika wa bi da'atika an ma'asiyatika wa bi fadlika amman siwak.' Juma'a biyar ba za ta zo wa mutum ba, sai ya wadata insha Allah.
TAMBAYA: Game da suratul Balad da kwanan baya Malam ya ce za a rika karanta ta da asuba, kuma har da rubuta ta, shi ne nake neman karin bayani a kan wannan. Abu na biyu kuma akwai wani bawan Allah da ya daukar wa kansa karanta Alamnashraha duk bayan sallar magariba kafa arba'in da daya shi ne nake son Malam ya dan fada mana falalar ita wannan sura.
DAKTA YUSUF ALI: Ita dai suratul Baladi, lokacin da muke yin karatu, to galibi wadansu abubuwan suna da yawan gaske, wato ka'idojin nata suna da yawa. Kuma na fadi abubuwa da yawa game da ita.Ba shakka akwai na maganar za a karanta kuma a rubuta a kyalle, kyallen ana iya yin laya da shi. Ko kuma na wanda za a rubutan a sha, amma dai na kyallen ne muka ambata. Kuma za a rubuta ne kafa daya kawai. Ka san kowane abu da muhallinsa, sai dai dukkan abin nan da muka fada akwai shi a rubuce, idan yana buktar su to akwai su a rubuce, sai ya zo ya kar~a.
Ita kuwa Alamnashraha, ana yin sallah ne raka'a biyu.Wato dai kowace irin bukata mutum yake da ita, musamman a yayin da mutum ya yi ta neman bukatu iri-iri kuma ya jarraba lakunkuna iri-iri. Kuma ya yi wasu dabaru da yake ganin bukatar za ta biya, amma ba ta biya ba. To a sannan ne ake amfani da Alamnashraha, kuma jimlarta shi ne kafa 152. Mutum bayan ya yi sallah raka'a biyu, wato Fatiha daya da Inna Anzalnahu a raka'a ta farko, sai ta biyu Fatiha da Izazul. Bayan sallama wato sai mutum ya karanta ita Alamnashraha kafa 152. To insha Allahu wannan bukata da ta wahala bai same ta ba, to da sannu Allah zai warware. Bayan wannan kuma akwai wani sirri da Allah ya sanar da ni, amma daga baya na ga Malamai sun fadi.
Wannan ya faru ne tun wajen 1970 ko da dan wani abu, an kawo ni in yi wa wani Yaro magani dan gidan wasu masu kudi ne sosai. Lokacin ina can Galadanci a gidan dan Lawal.To a wannan lokacin ne har ya kasance, wai ana ta labarina ne,don haka sai aka dauko ni in yi wa wannan yaro magani. To sai na karanta 'Alamnashraha laka sadarak' zuwa 'Innama'al usri yusra' kafa bakwai na tofa masa, na kuma karanta '{ulhuwallahu' biyar na tofa masa. Shi kenan kawai sai ya tashi, lokacin ma mutane masu zuwa duba shi ba su tafi ba, sai ga shi ma har ya dauki keke ya fita. Saboda haka tun daga wannan lokacin kuma kowace irin cuta in dai na karanta 'Alamnashraha' zuwa 'Innama'al usri yusra,' to sai ka ga an sami biyan bukata, da kuma wannan '{ulhuwallahu' din. Saboda haka tunda ya ce yana neman ladanin ne, to ga shi nan an ba shi. Kuma 'Alhamdu lillahi' yana da tasiri sosai. Wannan shi ne abin da zan ce.
TAMBAYA: Tambayata ita ce, a shari'a menene hukuncin yabanyar gona da aka shuka, shin menene hukuncin sai da wannan abu? Tambayata ta biyu ita ce akwai wata aya a cikin suratul Yasin 'Waj'alna min baina aidihim saddan wa min kalfihim saddan fa agshainahum fahum la yubsirun.' Akwai lokacin da mahaifina ya sami rashin lafiya ta shanyewar rabin jiki. To sai wani Malami ya zo ya ba mu wani magani cewa duk bayan sallar isha mu karanta masa, to a gaskiya na nemi wannan adadin na rasa don haka ne na ce bari in tuntu~i Malam na san da yardar Allah, Malam ba zai rasa sani ba.
A biyo mu mako na gaba in Allah ya kai mu.
Komawa babban shafinmu Komawa saman wannan shafin
|
|