Aliko Dangote: Labarina
A hirar, mashahurin Dan kasauwar ya yi tone-tone da ballake-ballaken asirin abin da ya kira da cuwa-cewar da a cewarsa ake tafkawa a kamfanin mai na kasa NNPC a takaice. Sannan kuma ya fadi irin tagomashin da ya ce ’yan Nijeriya za su samu daga sayen Matatun mai biyu na kasar nan da ke Kaduna da Fatakwal din da ya yi. Wadanda kuma sun jima da shiga cikin halin ha’u’la’i.
Wannan dai labari ne daga bakin wanda ake damawa da shi, ake kuma sha da shi a gidauniyar shirin cefanarwa da kuma mayar da kamfanoni da masana’antun gwamnati masu zaman kan su. Ba don komai ba kuwa, illa dandazon damin dukiyar da ya mallaka, wanda shi da kan bakinsa, kuma gabansa gadi, ya fada cewa ya yi wa matar nan, Oprah Winfrey, da aka ce ita ce bakar fatar da ta fi dukkanin bakaken fata kudi, a doron duniya fintin kau. A yanzu kuma haka, yana kan hanyar zama daya daga cikin giggan hamshakan attajirai ’yan kasuwa na duniya. Don baya ga mamayar da ya yi wa harkar kasuwancin sukari a ilahiri kasashen Afirka da ke kudu da Hamada, to ya kuma tsallaka zuwa Indiya da harkar kasuwancinsa, inda nan ma yake yin gagarumin tasiri ga tattalin arzikin kasar.
Duk kuwa da damin dukiyar da yake da ita, Alhaji Aliko Dangote, a cewar SUN din, in aka gan shi za a ga wani mutum ne kamar kowane matsakaicin dan Nijeriya, kai, in ma ba a ce talaka ba ne. Ma’ana, hamshakin mutum mai kama da rashin hamshakanci.
“Dangote tamkar littafi ne da ba za a iya fadar abin da ya kunsa ba ta la’akari da bangonsa, sai fa in an karanta.
Haji Aliko Dangote, a hirar, ya ce, shi iyakar abin da yake so shi ne kawar da fatalwar durkushewa, gazawa da kuma muna-munar da suka zama ruwan dare a manyan ofisoshin gwamnati. Don haka, a wannan labarin, Dangote ya fadi dangantakarsa da Obasanjo da kuma gwamnatinsa da ta gabata, da ma wasu gwamnatocin da suka shude. sannan kuma ya fede biri har jela dangane da burace-buracensa kan Nijeriya da kuma ’ya’yanta. Kana kuma ya yi fashin baki kan yadda ya mallaki matatun man kasar nan, da kuma burin da ya ce yake da shi game da fannin sarrafa siminti a Nijeriya. Kana kuma ya yi raddi ga masu cece-kuce kan sayar masa da matatun mai din da aka yi. Zance ne dai daga bakin mai shi. Ta sigar tambaya da amsa aka yi hirar, amma SUN ta kawo shi a sigar rubutun insha’i. Kasantuwar DILLALIYA na da kirari ‘GONARKI KASUWA’, ta ce to, ai da ma abin fada na masu baki ne. Dangote da rukunin kamfanoninsa kuma, kasuwancin suka kasa suka tsare. Don haka muka kawo fassarar hirar. Shin wanene DANGOTE? Meye rukunin kamfanoninsa ke yi? Ina suka sa gaba kuma yanzu? A dai bi labarin da karantawa kawai. A sha karatu lami lafiya:
KASANTUWATA NA DAYA
Labarina, labarin wani mutum ne da ’yan Nijeriya suka sani, suke so, sannan kuma suka marabce shi. ’Yan Nijeriya na tare da mu ne saboda amannan da suka yi da sunan Dangote. Baya ga amannar su da mu kuma, to muna fa da kyakkyawan tarihin da za mu iya nunarwa a ko’ina. In ka dubi masana’antunmu, to za ka ga cewa sun girmama ne gami da kankama sannu kan hankali, har kuma muka kawo matsayin da muke a yau. Saboda haka a matsayi na tawali’u, muna iya cewa mun yi kokari sosai. Babu wata harkar kasuwancin da muka shige ta da ba mu zama na daya ba. Wadanda kuma muka tabarbare a ciki ne kawai, za mu zo matsayi na biyu. Wannan kuma shi kan sa, dabararmu ce ta kasauwanci. Burinmu shi ne mu mamayi kasuwanninmu, mu zama mu ne ke jagoranci a fannin kasuwanci. Kuma dukkan harkokinmu, kwararrun mutane ne ke tafiyar da su bisa iyawa sosai. Mun kuma yi suna mai kyau, sannan kuma wannan ma wani bangare ne da ya jawo mana jama’a. Ba kuma wai suna sa kudadensu ga Aliko Dangote bane kawai, a’a, suna zuba kudinsu ne a kayan Dangote, saboda imanin da suke da shi kan hazikancin kasuwancina, amma kuma fa ba wai wannan ne kawai dalilin da ya sa suke zuba kudinsu ba. Don tunda farkon farawa, a ko da wane lokaci, mun kasance masu lura da kuma la’akari da abin da irin abin da mu ke ba masu tu’ammali da kayan mu. Domin in mutum ya fara saka da mugun zare, to fa ya gama kenan. Hasara kuma ta shiga. Don kusan ba zai yiwu ba ka dawo ka ce za ka gamsar da mutane.
Zama na farko kuma ba fa abu ne mai sauki ba, don ba a ko da wane lokaci ne muke kasancewa na farko ba. A galibin lokuta ma, muna farawa ne a matsayin masu kalubalantar wadanda suka riga suka yi mamaya a wani fagen. Alal misali, ka dubi lokacin da muka shiga kasuwa a shekara ta 2000, inda muka tarar da wasu da suka shafe shekaru 40 a fagen kafin mu mu shigo. Da muka shiga din kuma mun yi gwagwarmaya ne har muka zamanto na biyu a fagen. A yanzu kuma muna gab da zama ’yan sahun gaba a wannan bangaren. Hajar da muke sayarwa din kuma ita ce garin fulawa. Mun yi gwagwarmayar gabatar da kayayyakin Dangote ne inda muka rika bayar da mai inganci. Ma’ana muna da ikon gabatar da ingantacciyar hidima ga dukkanin masu sayen kayayyakinmu don amfanin kansu. Don kaiwa ga wannan ikon kuma, muna matsanancin zuba jari ga hakan. Baya ga zuba dimbin jari a wannan fanni kuma, muna tabbatar da cewa ingancin kayanmu ya dore a har kullum da irin ingancin da aka san su da shi a da, tun ma lokacin da muke shigo da garin fulawa.
A da dai shigo da kaya ne kawai aikinmu da kuma kasuwancinsu. Da farko kuma siminti muke sayarwa, amma yanzu mu ke yin sa a nan. A yau kuma siminti mafi inganci a Nijeriya shi ne namu – kana ma iya neman samfuri don kwatantawa – kuma wannan siminti yana fitowa ne daga masana’antar sarrafa simintinmu da muka kafa shi a kan kudi Dala biliyan daya a garin Obajana. A can din kuma muna da kashi 97 cikin dari na kayan sarrafawarmu da muke samu a cikin gida. Daga cikin abin da muke da karancin sa shi ne tsakuwar jifsum (gypsum) kawai. Shi din ma muna sayen wani bangarensa daga yankin Gombe mu hada da wanda muke sayowa daga kasashen waje. In banda wannan, komai yana nan tare a guri guda. Kuma simintinmu ne mafi inganci in aka kwatanta da wanda da muke shigo da shi daga Taiwan, Turai da kuma Sin.
Abubuwan da ke mana tsada kawai wajen sarrafa siminti sune aikin hako ma’adinai da kuma samun wadataccen wutar lantarki. Wannan ne ma ya sa ribar kafa masana’antar sarrafa siminti a Arewa ta karanta bisa wacce ake samu a Kudu. Domin kana da bukatar wutar lantarki mai yawa a Arewa. Alal misali, Ashaka kudin da ake kashewa a Ashaka da wanda muke kashewa a Obajana ba daya bane. Ko da ma za a yi amfani da mizanin tattalin arziki ne, yawan ma’aikatan da ke Ashaka sun ninka namu a Obajana da kimanin biyu da rabi ko kuma ma uku. Duk kuwa da cewa su suna samar da tan 750,000 ne, mu kuma muna samar da tan miliyan 5 a shekara. Saboda haka za ka iya ganin bambancin da ke akwai a wannan bangare. Dalili kuwa shi ne, mu muna da injuna na zamani da ke sarrafa kansu da kansu ainun, a tamu masana’antar. In ka dubi dakin kona garin simintinmu ba za ka taba ganin wani ba. Ba hayakin da ke fita da zai gurbata muhalli. Saboda haka muna zaune lafiya da muhalli a aikinmu. Kazalika kuma ba za ka ji wata kwaramniya ba. Za ma ka yi tunanin cewa an rufe masana’antar ce ba ta aiki, amma kuma muna ci gaba da aiki kullum. Sai dai kawai ka ga siminti na fita.
Sannan kuma ni kaina ba wani abu mai sarkakiyar ganewa game da ni. Illa iyaka dai kawai muna da kamfanin da ya dukufa ka’in da na’in a harkar kasuwanci. Duk da cewa ni ne babban Jami’in kamfanin, amma kuma gudanarwar fa ta hadaka ce; ba wai ni kadai ne ke tafiyar da kamfanin ba. Akwai sauran hazikai. Don in ban samu goyon bayan da ya dace ba, ba zan zama dan kasuwan da ke da basira ba, ballantana kuma har in kai wani wurin da na kai a yau. Dangane da batun ci gaba kuma, mun dai samu dimbin nasarori kam a cikin shekaru uku kamar yadda ni na yi imani, amma in lokacin da muka kammala manyan ayyukanmu da ke kasa yanzu ya yi, to za mu zama kamfani mafi girma a Afirka.
DANGANTAKATA DA GWAMNATI
Babu wani mutum a duniya da zai zuba jaruka ya zama kuma yana fada da gwamnati. Kuma ko da a ina ne kake, walau a Rasha ne, Birtaniya ne, ko ko Amerika. Ba za ka zuba jari ba kuma ka ce, to madalla, babbar abokiyar gabana ta farko ita ce gwamnati ba. Shin mutanen da ke zargi na da kasancewa mai dasawa da gwamnatin Obasanjo na zaton in ce babbar abokiyar gabana ce gwamnati? Wannan ba shi yiwuwa. Kai, babu wata harkar kasuwanci ma da ba ta da alaka da siyasa. Babu wannan sam. Ina kuma kalubalantar duk wanda ke ja da ni. Domin zabi biyu ne kawai; walau ka ce da gwamnati “madalla, ina tare da ke,” ko kuma ka ce, “faufau ni mai hamayya da ke ne.” Amma kuma a zahiri, mutumin da ke da kyakkyawan tunani, cewa zai yi, ni ina tare da ke. In kana da bukatar gwamnatin kasar da kuma mutanenta kenan, to wannan ne zabin abin da za ka yi. A nan ne kuma batun tafiyar da sha’anin mulki tare, da kuma na sauke nauyin tsarin zamantakewa ya taso. In ba kana son kalmashe hannayenka bane ka kuma zuba ido kawai, alhali kuma kana gudanar da harkarka a wannan muhallin da gwamnatin ke mulki. To in kuma kana gudanar da harkarka a wannan muhallin da take mulkin, me zai sa ka ce gwamnatin ce abokiyar gabarka?
A matsayinka na dan kasuwa, a ko da wane lokaci ka zama mai bai wa gwamnatin shawarwari. Ya kamata ka gaya mata cewa e, kaza daidai ne, kaza kuma ba daidai bane. A duniyar da ta ci gaba ma, a hakika, ba gwamnati ce ke gudanar da tattalin arzikin kasa ba, bangaren ’yan kasuwa masu zaman kansu ne ke tafiyar da shi. Amma kuma wajibi ne a samu hadaka ta kwarai a tsakanin gwamnati da kamfanoni da masana’antun da ke zaman kansu. In kuwa bangaren kamfanoni da masana’antu masu zaman kansu na ma juna kallon hadarin kaji, to sha’anin tattalin arziki ma ba zai je gaba ba. Don haka suna da bukatar wannan kyakkyawar fahimtar junan don samun cilla tattalin arziki gaba. A nan ne kawai muka kasance a matsayin gada mai sadar da kowane bangare. In da a ce ina da wannan harkar kasuwancin, sai kuma na kama mukamin Minista, to a nan ne kuma lamarin zai sauya kwata-kwata. Wannan kuma ba wai ina alfahari bane, a’a, mu harkar kasuwancinmu ta hakika ce. Hakika da ma’anar cewa, e, muna da harkar kasuwancin siminti da ita, alal misali. Ita kuma wannan harkar kasuwancin simintin da muke yi da ita, duk gwamnatin da ta zo ma za mu dasa da ita, domin da ma muna dasawa da gwamnati. Na farko kenan.
Sannan kuma ina da imanin cewa duk wani kamfani a duniya yana dasawa da gwamnati. In ba haka ba kuma Jim Ovia ya mayar da gwamnati abokiyar gabansa mana, ka ga inda bankin Zenith za shi.; ko kuma bankin UBA, ko bankin First Bank. Su ce ba su ba gwamnati mana, su zaman kansu suke yi. Su fito mana su fadi abubuwan da suka saba wa gwamnati. Da kuwa sai su san cewa taka kunama ba gam da katar bace.
TSAKANI NA DA OBASANJO
Dangantakata da tsohon Shugaba Obasanjo ta ginu kawai a kan asasin cewa shi Shugaban yana son mutanen da za su kara gwababa tattalin arziki. In da ko ban kasance mai kara gwabi ga tattalin arziki ba, to ina tabbatar maka da cewa da ban kasance mai dasawa da Obasanjo ba. Don kashi 85 cikin 100 na dangantakata da Obasanjo na da nasaba ne da abin da ya shafi tattalin arzikin kasa. In har aka ga mun zauna tare, to kashi 85 cikin 100 na zaman na tafiya ne kan maganar abin da ya jibanci tattalin arziki. ma’ana yaya za mu yi mu ci gabantar da tattalin arzikin? Sannan kuma ni, ina jin ya kamata in yi godiya kan hakan. Bari ma dai in dan gaya muku wata magana, in da ba don karfafawar gwiwa da kuma angizo daga Obasanjo ba, da masana’antar sarrafa simimti na Obajana ba ta kafu ba ko kusa. Saboda haka angizon sa ne ya sa muka samu kaiwa ga burinmu. Da sai ma in fi samun kudi sosai daga shigo da siminti daga kasashen waje, don ni na san abin da nake kashewa ga hakan, saboda haka sai in zame ribata daga masu saye kawai. Sannan kuma a yau din nan, kudin dauko kaya daga kasashen Asiya zuwa nan, abin ya wuce hankali. Da hakan ake yi kuma, da mutane sai sun rika sayen buhun siminti a kan kudi fiye da Naira dubu biyu, inda shigo da shi din za a yi. A yanzu din nan kuma (lokacin da ake wannan hirar da Dangote) ina kan hanyata ce ta zuwa ganawa da Gwamnan jihar Ogun, don muna son yin abin da muka yi a Obajana har sau biyu a jihar, wato Shagamu da Igbese. Kuma tabbas za mu kattaba hannu a kan yarjejeniyar kwangilar a cikin wannan watan, sannan kuma dan kwangilar zai je filin da za a yi aikin ya fara aikin share flin cikin kwanaki 90. Da ma mun taba yin irin wannan aikin a wani lokaci a baya, amma na yanzu zai ninka na baya har sau hudu, kamar yadda muka yi niyya.
Game da Obasanjo kuma dai, bari in gaya muku wani abu. Ba mu taba kulla wata harkar kasuwanci da wani da ke cikin gwamnati ba ko kadan. Ba na son yin alfahari, amma dai bari in gaya muku wani abu kuma dai. An haife ni ne a cikin kudi. Amma ta bangaren iyaye na maza – da kuma bangaren iyaye na mata sun kasance masu kudi ne a har kullum. Saboda haka ba wai na girma ne na tsinci abin haka kawai ba. Amma kuma wannan ba ya nufin cewa kowa da kowa a dangina mawadaci ne. Ban san wani mutum ba, walau daga bangaren mahaifiyata ko daga bangaren mahaifina da ya taba kulla wata huldar kasuwanci da wani mutum da ke cikin gwamnati ba. Don haka ba ma Obasanjo ba, ko da a cikin al’ummar nan ba mu da wani da muka yi wata hadaka da shi.
Dangane da sabuwar masana’antar sarrafa simintin da za mu kafa a jihar Ogun kuma, muna sa ran mu rika sarrafa tan miliyan goma ne a duk shekara a nan. Yanzu kuma abubuwa sun yi tsada, ko da kuwa a kasashen waje ne. Saboda haka, kudin aikin gina wannan masana’anta kuma shi ma zai haura kenan da kamar kashi 40 cikin 100, amma gogewar da muka samu a masana’antarmu ta Obajana za ta sa mu yi su a adadin kudin da muka kashe a can da. Saboda haka, a jihar Ogun, muna sa ran zuba jarin Dala biliyan biyu, sannan kuma muna da sauran Dala miliyan 850 da za mu zuba a masana’antar Obajana. Don akwai wasu sassan da ke neman wannan rarar, kamar fannin samar da gidaje, za mu sa masa dan kadan, sai kuma bangaren sanya bututun gas da ba mu ma yi wani abu tukuna a kai ba. Don za mu kashe Dala miliyan 850 don samar da tan miliyan 10 na siminti a shekara. Sannan kuma burinmu ne mu rika samar da tan miliyan 23 a kowace shekara a matsayinmu na rukunin kamfanonin Dangote kawai. Alabasshi kuma sauran mutane sa rika samar da sauran tan miliyan biyar din da suke bukata.
Ma’ana a nan za mu zuba jarin kimanin kashi 30 zuwa 35 a cikin 100 na kudaden. Daga nan kuma sai mu nemo rancen ragowar kashi 70 din. Za mu kuma nemi wannan rance ne galibi daga Hukumar samar da rancen kudade na duniya, IFC a takaice, wacce take bangare ne na bankin duniya. Sannan kuma za mu ranta daga bankin bayar da rancen zuba jari na kungiyar hadin kan Turai, wato EIB a takaice. Sannan kuma za mu tuntubi wasu bankunan kasashen waje da namu na gida. Saboda haka a jimlace, za mu kashe wannan adadin kudin ne daga yanzu ya zuwa shekarar 2010. Sannan kuma ina mai tunatar da ku cewa muna fa da harkokin kasuwancin da ke ci gaba da gudana, wadannan harkokin kasuwancin kuma ba wai kanana bane, gigga ne sosai. Saboda haka za mu iya biyan wani bangare na kudin da kanmu. A bangaren sarrafa siminti kuma, daga cikin Dala biliyan 2 da digo 85 din da muke da shi, ina jin gudummawarmu itace dala biliyan 840, wanda shi ne kashi 30 cikin dari na jimlar kudin. Don haka a cikin harkokinmu, muna da isassun kudin da za mu yi aikin ginin masana’antar da shi. Sannan kuma kar ka manta, za a yi aikin ne cikin shekaru uku. A cikin wadannan shekaru kuma harkar kasuwancinmu yana ci gaba da samun riba ne. Kenan mun yi amannar cewa muna da kudin, za mu ci gaba kawai da wannan aikin ne.
ABIN DA YA SA NA SHIGA KAFA GIGGAN MASANA’ANTU
Kalubalen da ke tattare da wadannan giggan ayyukan kafa manyan masana’antun, da kuma dimbin makudan kudaden da za su lashe wadanda suka kai biliyoyin Daloli ko kadan ba ya tsoratar da ni. Dalili kuwa shi ne, in mu ba mu yi ba, ba fa wanda zai zo nan ya yi mana shi a nan Nijeriya. Bari ma dai in maka bayani filla-filla kan abin da ya sa muke zuba manya-manyan jaruka a nan, musamman ma dai a bangare guda, wato sarrafa siminti. A matsayina na dan Nijeriya, in so in tabbatar da cewa, duk inda jama’a ke zama, in dai ba wani guri ne surmukukin da ba ya shiguwa ba a nan kasar, to ina son in ga cewa ana sayen siminti a farashin da bai haura Naira 1000 ba a buhu guda. Abin da nake nufi a nan shi ne cewa duk da farashin safara da duk wata ribar da mutane za su samu, ba zan sai da simintin a farshin da ya haura Naira 800 ba a buhu guda. Ina son karya tunanin da mutane ke da shi na cewa da zaran farashin kaya ya haura, to fa ba ya saukowa kuma. Ina kuma jin cewa in har muka kammala wannan shirin da muke da shi a shekarar 2010, to, farashin siminti zai yi kasa sosai. Wasu mutane suna cewa abin da muke yi shi ne sake ma simintin duri, amma ba sarrafawa ba. Sai dai in yi dariya kawai. Abin da nake son mutane su yi kawai shi ne su ziyarci kamfanin sarrafa simintinmu da ke garin Obajana, inda a kullum tirela 300 ke fita shake da lodin siminti. ’Yan gaza gani ma su zo su gane ma idonsu ko za su ga ana shigar da siminti, in kuma ba su gani ba, to za su ga kuma simintin ne ke fita a kullum. A kasuwa ne ma bai ba da wata ma’ana ba a ce mutum ya dauki simintin ya kai shi Obajana ya sake masa duri. Sannan kuma inda muke hako dutsen yin simintinmu ma na nan kusa, sannan kuma jama’a za su ga irin abin da muke fitarwa daga kasa. Da zaran kuwa ka ga haka, to za ka san cewa muna kara ma tattalin arzikin kasar nan kima. Masana’antar Obajana kadai a yau ta sa kasar nan na tsimin kudin da ya kai rabin biliyan na Dala. Wala’alla kuma, a yau hakan ba zai ba da ma’ana ba, amma kuma gobe, in farashin danyen mai ya fadi kasa daga dala 40, to a nan ne masana’antu irin su Obajana za su ceto Nijeriya. Domin ko muna da mai, ko ba mu da shi, dole ne dai mu rika shigowa da siminti don mu samar da gidaje. Sannan kuma siminti na daya daga cikin muhimman kayayyakin da dole gwamnati ta tabbatar ana da wadatar sa.
Na biyu: In kuma suka ce muna sauya ma sukari ma buhu ne, to nan ma mutum na bukatar ziyartar masana’antarmu a Apapa don ya ga wane irin sukari muke shigarwa. Abin da muke shigarwa shi ne danyen sukari wanda ba ya yiwuwa dan Adam ya sha shi. Sannan kuma ba mu kadai bane ke da masana’antar sarrafa sukari a duk duniya. Akwai masana’antun sarrafa sukari, da dama a duniya, amma kuma akwai manyan kasuwannin sukari biyu. In ka dubi nau’o’in sukari, za ka ga cewa muna da wanda ake ce ma London No 5, wanda yake fari; sannan kuma sai nau’in New York No 11, wanda kuma danyen sukari ne shi, farin kuma ya sha bamban da shi. Wannan shi ne abin da akasarin mutane ba su fahimta ba. Muna samo danyen sukari ne mu tace, mu ware ainihin sukari daban da sinadarin molasses. Inda za ka je kamfaninmu a yau za ka ga cewa harkar kasuwancinmu ba na sayar da sukari bane kawai, a’a, har ma da sinadarin molasses. Sannan kuma muna da wani dagwalon da ake samu daga sukarin, wanda kuma yake da amfani ga gona. Wannan dagwalon ne dai kawai ba mu da kasuwarsa sosai.
LABARIN SANA’AR SUKARI
A yau din nan, in da sake durin sukari kawai muke yi, to me zai hana in je Ghana ma in yi hakan? A yau kuma ina rubanya yawan sukarin da masana’antata ta sarrafa sukarin ke samarwa don a rika fitar da shi zuwa kasashen waje. Me ya sa? Saboda kungiyar hadin kan Turai, EU a takaice, ba ta yi nasara ba a shari’ar da ta yi da kungiyar kasauwanci ta duniya, WTO a takaice, kan yadda take jibge sukarinta a wasu kasashen. Wadanda suka shigar da karar kuma sune Brazil da Thailand, kuma sun yi nasarar karar. Inda kuma ita EU din ta daukaka kara, amma ta sake faduwa. To, kasantuwar rashin nasararta a daukaka karar da ta yi ne ya sa dole ta bayar da fili ga wasu kasashen. Don haka madalla da hakan, yanzu kasashen EU din ba za su iya fitar da sukari zuwa kasuwannin kasashen duniya ba; a da dai suna fitar da sukarin da ya kai tan miliyan 7 da digo 23 ne, amma daga nan kuma, wato daga shekarar 2006 ya zama suna iya fitar da sukari tan miliyan 1 da digo 23 ne kawai. Wannan na nufin an samu tazarar tan miliyan 6 kenan. Wannan ne kuma ya sa mu ma za mu rubanya sana’armu ta samar da sukari, don alal akalla mu iya kame kasuwannin Afirka. Wannan tazarar da aka samu kuwa ya shafi ko’ina a duniya, amma dai ya fi tasiri ne a kasashenmu na Afirka da wasu na Asiya kawai. Da ma kuma su kasashen tarayyar Turai din na samun kasuwarsu ne a Afirka gaba daya, musamman ma dai arewacin Afirka da kuma Nijeriya, kasantuwar muna shigo da sukari mai daman gaske. Amma yanzu mun samu tazarar tan miliyan 2 a kasashen Afika da ke kudu da Hamada. Wannan ne ma ya sa muke ta kara fadada harkarmu a wannan fanni. Don mu ma ba wawaye bane. Wannan kuma shi ne babban dalilin da muke da shi na kara zuba jari a harkar samar da sukari ka’in da na’in a masana’antarmu, inda muke son mayar da ita mafi girmar masana’antar sukari da guri guda da take sarrafa sukarin da ya kai tan biliyan 2 da digo 5 a shekara daya.
Na san kasashen Yammacin Turai na iya yi min zagon kasa, kasantuwar an sa su rufe masana’antunsu na sarrafa sukari. Tunda ko suna rufe masana’antunsu, to me za su rika fitarwa zuwa sauran kasashen duniya kenan? Kenan ba zai zama muna gasar kasuwanci da su ba. Babu sauran gasa mu da su. Inda za mu yi gasayya ne, to ka ga wannan wani abu ne kuma daban. Yanzu ma sun mayar da akasarin gonakin rakensu na wasu abubuwan daban. Wannan kuma wani batu ne da kwata-kwata ya bambanta da wannan. In kuma aka hanga gaba, za a ga cewa akwai karancin masana’antun sarrafa sukari, kamar dai yadda lamarin yake a bangaren mai. Wannan karancin ne kuma yake kawo haurawar farashi sama kasantuwar ana da bukatar samar da kayan fiye da abin da ake iya samarwa. Don mutane ba sa zuba jari a harkar tace mai sosai a shekaru 20 zuwa 30 da suka gabata. To haka ma lamarin ya kasance a sha’anin sarrafa sukari. Shi danyen sukari, in aka duba za a ga cewa yana da araha sosai, amma masana’antun sarrafa shi ne aka rasa.
TUNANIN MUTANE SHI NE IYAKARMU CIKIN NIJERIYA
Mutane na da tunanin cewa iyakar harkokin kasauwancinmu cikin gida Nijeriya ne kawai. Suna kuma da tunanin cewa kamfaninmu wani dan karami ne kawai, da bai zarce nan cikin gida ba. Sannan kuma matsalar ’yan Nijeriya ita ce cewa wai mun zama na daya ne kawai saboda surutan da muke yi. To, saboda irin wannan tunani ne muka dan yi gum na wani lokaci gwargwadon yadda ya samu. Mu ba masu surutu da hargagi bane. Kuma, bisa la’akari da inda na fito, ba a koyar da mu surutu da hayagaga ba. An dai koyar da mu da mu zama masu tawali’u da saukin kai. Babu bukatar mu koda kanmu da kanmu. Sai dai wasu dai su koda mu. Alal misali, gwanin wasan kwallon kafa ba ya fitowa ya ce shi dan wasa ne na kwarai. Sai dai ya je fagen wasa ya tabbatar da cewa shi gwanin ne. A nan ne in mutane suka ga abin da kake yi kuma, sai su ce, “kai, wannan gwani ne.” Saboda haka ba ma bukatar yin ihun kururuta kanmu. Ba kai ne za ka tallatar da kanka ba a wasu lokuta, wasu ne za su tallata ka. Don haka mu ma yadda muke kenan. Saboda haka da yawan mutane ba su fahimce mu ba, ba su san inda muka dosa ba, amma dai, muna kara ma tattalin arzikinmu kima. A wasu lokuta mukan ga koken mutane na cewa Dangote wannan ne, a’a Dangote wancan ne, Dangote kaza ne, amma kuma sai suka manta da cewa mun shafe shekaru 28 cur muna aiki ba yankewa. Ba mu ma taba nuna wata gajiyawa ba tun daga ran da muka fara, aiki kawai muke ta yi tukuru. Don haka mun san burin da muke son mu cimma, mun kuma san inda muke son kaiwa. In kuma ba mu yi hakan ba, ’yan Nijeriya ba za su shiga a dama da su, a kuma sha da su ba a tattalin arzikinmu.
A halin yanzu haka muna kan tattaunawa da wani iyalin kasar Indiya don mu sayi kamfanin sarrafa simintinsu. Wannan kamfanin simintin kuma ya rubanya kamfanin simintinmu na Obajana fiye da sau biyu. Muna kuma fatan samun nasarar yin hakan. Mutane ne kawai ba su fahimta ba a hakika. da zaran ka kai wani matsayi, to samun kudin ba zai zame maka wani abu mai wahala ba. Wannan kuma shi ne matakin da muke kai a yanzu. In ka ji cewa muna aiwatar da wani babban aikin da zai ci kudin da ya kai Dala biliyan 4, sai ka ji wani ya ce, daga ina za ka samu kudin, alhali kai dan Nijeriya ne? Mukan ce, e, za mu samu kudin. ba wai lallai ya zama 100 bisa 100 kudina bane. Bankuna fa sun yi amanna da hazakata, sun kuma yi imani da iyawata ga yin abubuwa, don haka su ma suna kawo dauki. Idan suka ga tsarin lamarin, sai su ce kana da kashi 20 ko 30 cikin 100? Sai in ce, e, ina da shi. Shi kenan sai su ba ka kudi. Shi kenan an gama. Saboda haka suna bukata ta. Sannan kuma in babu hamshakin dan kasuwa na gari, to duk kudaden banki za su yi tasgaro ne kawai. Domin su ba su da bukatar kudin. Su dai aikinsu kawai shi ne su tabbatar da cewa kudaden sun haifar da riba mai inganci. Wani abu kuma da za a lura da shi a nan, shi ne cewa dan kasuwan da ya gabatar da irin wannan bukata ta aiwatar da wani babban aiki, ya zama ya san takamaimen abin da yake magana a kai. Zan iya tunawa da cewa lokacin da muka gabatar da bukatar aikin kafa kamfanin sarrafa siminti na Obajana, sai wasu bankunan suka yi tambayar cewa: Wannan zai yiwu kuwa? Shin wannan manufa aiwatacciya ce? To, amma ga hamshakin dan kasuwa, komai kan somo ne daga tunani, wanda daga bisani kuma zai zama na zahiri.
BAYAR DA RANCE GA TALAKAWA
Ba shakka bankuna na da gagarumar rawar takawa a kowane tsarin tattalin arziki. Su, suna aiki ne a matsayin masu shiga tsakani a kowace harkar kasuwanci. Saboda suna taimakawa ne ga hamshakan ’yan kasuwa da kudaden jari. Bankunan Nijeriya ma sun jima suna yin haka. Ni kuma shaida kan hakan. Sai dai akwai wani bangare guda da ba na jin dadin sa. Wannan bangare kuwa shi ne na bayar da kankanan rance ga talakawa. Wannan bangare kam, a yanzu, muna da bukatar sauya shi. Kasantuwarsa na cewa ba a janibin aikin bankunan ya kamata ya kasance ba. Dalili kuwa shi ne, ba su da kwarewar gudanar da wannan harka ta bayar da kankanan rance. Saboda haka, muna da bukatar wata tawagar musamman ta dabam, da su ne za su rika taimakawa ga gudanar da wannan harka ta bayar da kankanan rancen kudade, wanda hakan ne kuma zai bayar da taimako gagarumi ga tattalin arziki. Domin duk mutumin da ke kauye, in ka ba shi rance Naira dubu 50, to zai iya sauya rayuwarsa, amma kuma sai ya kasance, a hakika samun karamin rance ba abu bane mai sauki. Duk kuwa da cewa zai iya ba ka damar samun jari. ’Yan Nijeriya kuma ba ragwage bane bisa ga dabi’a. Suna da ruhin son kage-kagen abubuwan da za su taimaki kansu ainun, sai dai ba su da hanyar samun kudade ne kawai. Abin da nake nufi da samun kudade a yau shi ne cewa samun manyan kudade. Inda kun ziyarce ni ne a shekaru hudu baya, to da ban yi magana kan wadannan manyan ayyukan kafa masana’antun da na yi kan su a baya ba. Saboda haka in ba ka shiga an dama da kai ba, to ba za ka iya ci gabantar da tattalin arzikin ba. Sannan kuma babban bambancin da ke akwai, shi ne a matsayinmu na rukunin kamfanonin Dangote, ba mu boye kudadenmu a kasashe waje ba ballantana mu dawo gida ‘mu zauna mu zuba ido.’ A’a, muna shiga ana damawa da mu yadda ya dace. Kazalika kuma ba za a sa ran cewa lallai sai mun tafi da kowa da kowa ba a matsayin abokanmu. Amma kuma abu ne fayyatacce cewa mutum zai yi abokai na kirki, a lokaci guda kuma ya samu rundunar makiya. Su kuma za su yi ta ma hayaygaga da hargagi, amma hayagaga da hargaginsu ba zai dakatar da mu daga abin da muke yi ba.
Wasu mutanen na ta yin tambaya cewa me zai sa ba zan yi banki ba, kamar yadda wasu mawadatan ’yan Nijeriya ke da bankuna a matsayin wani bangare na fadada harkar kasuwancin su? Amsar da nake bayarwa ga masu irin wannan tambaya ita ce, ni ba kwararren masanin harkokin banki bane. Sannan kuma ba shi ne kashin bayan harkar kasuwancina ba. Harkata, a hakika, ita ce kakkafa masana’antu da kuma gudanar da su. Ni dan kasuwa ne kawai, ba masanin harkar banki ba. Kuma a matsayinka na dan kasuwa, abin da ya fi ma shi ne ka tsaya ka tafiyar da harkokin kasuwancinka kawai ya fi ma tafiyar da banki. Saboda haka ni hamshakin dan kasuwa ne da a kullum yake binciken fursoshin fadada kasuwanci. Abin da kuma nake nema shi ne gwababuwar kasuwanci da kuma kafa giggan masana’antu, kana kuma da samun jama’a. To, na yi iyakacin iyawata kenan. Saboda haka ba zan bayyana dukkanin asiran ba, sai dai wadannan ne kawai kadan daga cikin abin da nake nema.
MAKIYANKA MA KAN SAYI KAYANKA
Da farkon farawa dai a kullum ina mai imani da cewa kula da harkar kasuwancina ba wai yin hadakar kasuwanci ba. Me kuma zai sa ba zan so hadaka ba, musamman ma dai a Nijeriya? Ina ma iya gaya muku kai tsaye cewa hadakar kasuwanci ne hanya sassauka ta yakar kasuwancin kan sa. Akasarin ’yan Nijeriya, a hakika ma ba su fahimci ko me hadaka ke nufi ba. A yanzu kuma ba na son kowa, don in na yi hadaka da kai, matarka za ta soma gaya ma cewa, “Aliko fa ya sayi sabon jirgin sama, shin ma kana da tabbacin cewa ba zaluntar ka yake yi ba kuwa a kasuwancin da kuke yi da shi?” Saboda hakan ya faru ne, kana ma iya zuwa a matsayin kashin kanka ka tambayi wasu daga cikin masana kan harkokin banki din nan. Sun zuba kudaden hadaka sun kafa banki. Ka ce: Kun taba samun sabani da abokan hadakarku? Za su ce maka e, in za su fada ma gaskiya. Amma mu mun magance wannan tarnakin ta hanyar bude kofarmu ga kowa da kowa. Don haka ne ma muke sayar da hannayen jari ga jama’a. Da ma in ka bude kofar kasuwancinka ga kowa, to ko da ma makiyinka ne zai iya zuwa ya sayi hannun jari a kamfaninka. Don ba wani abu da zai hana shi sayen jarin a cikin kamfaninka din. Amma a gurina, hadaka daya rak nake da shi da kamfanin Blue Star Consortium, amma kuma ma mune ke da mafi rinjayen jarin kamfanin, saboda haka mu ke jagorantar sauran tawagar mutanen da ke da jari a kamfanin, saboda amanar da suka ba mu. Wannan ne kadai. Sannan kuma za mu kara ma kamfanin armashi da gwabi kwatankwacin wadanda muka yi ma kamfanin sarrafa siminti na Binuwe. Kazalika kuma mun kawo irin wannan gwabin ga kamfanin NASCON. Sannan kuma a yanzu mun samar da miloniyoyi da yawa daga kamfanin sarrafa sukari na Dangote (Dangote Sugar). Don a yanzu haka muna da mutum dubu dari da ashirin masu hannayen jari a ciki. Abin da ya sa muka yanke wannan shawara ta yin haka kuwa, shi ne muna son raba garabasar da ake samu ne da sauran jama’a. Sannan kuma wata manufa ta yin haka ita ce mu bayar da dama ga kamfanin ya kara bunkasa. In da a ce batun na neman hanyar samun kudade ne cikin sauki, to da sai mu tunkari bankuna kawai. Don ba ko shakka, kasuwancin jari ya fi tsada in aka kwatanta da neman rance daga banki. A lokacin da mutum ya zuba kudadensa ya sayi jari, to hakan ya ma fi tsada. Saboda haka zuwa banki neman rance ma ya fi sauki, a maimakon samar da kudade ta hanyar kasuwancin jaruka. Dalili kuma shi ne cewa jama’a za ta doru a kanka ne, saboda batu ne na kudi, ashe kenan sauki ne ma gare ni in nemi rance kawai daga banki. Don duk ribar da nake bayarwa ga masu hannun jarin nan, in rance na samu daga banki, to ribar tawa ce ni kadai dari bisa dari, ka ga hakan ya fi min da a ce in sayar da hannayen jari daga kamfanina kamar in je dandalin Tunibu Square ne in yi ma kaina da kaina terere. Don a yau din nan, mayar da kamfani gaba dayansa cewa kowa da kowa ma na iya mallakar hannun jari a cikin sa, to wajibi ne mutum ya zama kaifi daya a kowane al’amari. Don ko me ya faru, to labudda ka yi ma jama’a bayani a kai daki-daki game da shi, haka kuma abin yake. Amma kuma duk da haka, za mu ci gaba da shigo da jama’a dai, don ina so ne ’yan Nijeriya su amfana da basirata ta fuskacin kudin da nake samu. Amma a marhalar da ake ciki yanzu, alal hakika ba mu fara gabatar da komai ba tukun. Ina kuma ba ku tabbacin cewa akwai mu da wasu kamfanonin da za su fi samar da riba fiye da na kamfaninmu na sarrafa sukari, nesa ba kusa ba. Amma a yau, insha Allahu, in kuka duba karshen shekara, lokacin da za mu tattara sakamakon harkokinmu na sarrafa sukari, to ina ba ku tabbacin cewa za ku ga cewa harkar sarrafa sukari ce za ta zama mafi riba a kan kowanne.
YADDA NAKE TAFIYAR DA RUKUNIN KAMFANONIN DANGOTE
Dukkanin kamfanonina, kowanne na aiki ne a matsayinsa na mustakillin kansa, wani ba shi da alaka da wani. Ma’ana, kowane kamfani na da hukumar gudanarwarsa ne. Sai dai dukkansu wannan ofishin nawa na Lagos ne babban hedikwatarsa yake. Abin da muke yi a nan kuma shi ne lura da kuma sa ido ga yadda kowannensu ke tafiyar da lamarinsa. Don haka dawainiyar da ke kanmu ita ce tabbatar da cewa kowannen su ya yi abin da ake son ya yi. Kowane kamfanin kuma na da kasafin kudinsa, kuma a kan wannan kasafin ne muke gudanar da harkar kowanne daga cikin su. Illa dai kawai akwai wadansu abubuwan da muke tafiyarwa a hade. Wadannan abubuwa kuwa sune kamar lamarin shari’a, kula da ma’aikata, da kuma tambarin kamfani. Wadannan sune kawai abubuwan da ke a hade. Alal misali, kamfani kamar na Obajana, wanda muka zuba wa jarin biliyoyin Daloli, tun daga ranar da muka halarci bikin bude shi, to ban sake zuwa gurin ba. Domin da ma budewar ce kawai da kuma samarwa da mutane siminti, to kuma ana sayarwa, muna kuma kirga kudadenmu a kullum. Saboda haka ba na ma bukatar in je gurin. Amma dai muna ganin duk abin da suke yi. A inda muka ga za su kauce daga hanya kuma, sai mu dawo da su kan tafarkin da ake tafiya daidai-wa-daida bisa la’akari da ka’idodi. Da yake kuma muna kara samun ci gaba da habaka, saboda fadaduwar da nake yi zuwa wasu sassan a wajen Nijeriya, to akwai shirin samar da wani babban Jami’in da zai rika kula da rassan da ke fadin duniya, wato CEO kenan a takaice; inda Nijeriya ma za ta zama daya ne daga cikin rassan kamfanonin Dangote da suka yadu a kasashen duniya. Kuma a yanzu haka mun bazama kasuwannin duniya ne muna neman wanda zai zame mana CEO din mu da zai lura mana da Nijeiriya, Ghana Tanzaniya, da kuma Moroko. Bayan mun samu wadannan manyan Jami’ai ne kuma da za su rika duba mana wadannan kasashe, to daukkaninsu za su zama kafada da kafada ne da da CEO din mu na Kanfanin simintin Obajana, amma kuma dukkansu zai zama suna karkashin shugabancin babban Shugaba guda daya ne. Kazalika kuma za su rika mika rahotonsu ne ga wannan babban Shugaban. Shi kuma zai samu hukumar gudanarwarsa, wanda ni ne zan zama Ciyaman kuma ga wannan Hukumar gudanarwar.
Amma wannan CEO din da nake nema ba lallai bane ya zama wanda yake da kwarewar harkar tafiyar da kamfanin siminti – amma dai hakan karin wata fa’ida ce. Kana iya zama wanda ke da gogayya a harkar masana’antar mai, ya dai danganta da abin da ka samu gogayya a kai. Mu kuma za mu duba mu ga cewa gogayyar shekaru nawa ka samu. Amma kafin nan kuma, sa ma muna da kamfanin da ke yi mana wannan aikin. Yanzu kuma muna fafutikar farautar samun mutanen da za su yi mana shi. Yanzu kuma muna tattaunawa da wasu mutane daga wasu manyan kamfanonin siminti a wasu sassan duniya, don mu jawo su su kawo basirarsu da kwarewarsu ga namu kamafanin. A wasu lokutan ma nakan shiga da kaina cikin sha’anin daukar ma’aikata. Hakan kuma yana danganta ne da irin aikin da za a ba wanda za a dauka din. Saboda haka, batun daukar CEO kuwa, bayan sun jera sunayen kamar mutum uku zuwa hudu, to ni sai in shiga cikin lamarin, don tattaunawa da wadanda aka bayar da sunayen nasu. Don na san zai iya tambayata cewa menene mahangata? Menene kuma nake son in cimma. Ma’ana dai zai min tambayoyi shi ma kamar yadda zan masa tambayoyi. Wannan abin shi ne zatona.
Karin azama na daga cikin muhimman abubuwan da kan kai kowace harkar kasuwanci ga nasara. Don haka ne ma muke bayar da garabasar musamman ga wanda ya yi aiki tukuru. Tunda kuma za mu zama kamfanin da jama’a za su iya mallakar hannayen jari, to ma’aikatanmu ma za su zama masu hannun jari a kamfanin. Fa’idar da ke tattare da sanya ma’aikata ma su zama masu hannun jari a kamfanin shi ne cewa da zaran an samu wata ’yar matsala ko almundahana; kuma ma’aikata suka gano haka, sannan kuma suka san cewa su ma fa suna da jari a kamfanin, to za su ankarar cikin gaggawa, mamakon yin gum da bakinsu. Don shi cin hanci da rashawa kuma wani abu ne da za a ci gaba da yaki da shi ba dainawa. Sai dai kuma ba ina cewa ba mu da wannan matsalar bane a kamfaninmu, muna da ita. Don a ko da wane lokaci za ka ga cewa akwai mutanen da suke jin cewa suna da wayo a cikin kamfanin. Amma ni abin da na sani kawai shi ne cewa neman ci gaba ne zai tamaki mutum. Matukar kana da ingantattun matakai na kasuwanci a kamfaninka, ka tsara komai a na’ura mai kwakwalwa, sannan kuma daki-daki, to hakan zai taimaka wajen rage irin wadannan abubuwa. Amma kuma batun gamawa da shi gaba daya kam wani abu ne da kusan ba shi yiwuwa. Dalili kuwa shi ne cewa gaskiya ce cewa akwai matsananciyar zamba cikin aminci a Nijeriya. Sai dai kuma daya daga cikin irin abubuwan da suka dame ni game da wasu ’yan Nijeriyan – yanzu fa ba ina magana bane a kan kamfanina ba – sai ya zamana ce cewa su niyyarsu kwata-kwata daban ce. Kuma ko ka ce ma mutum ya rubuta ma kansa da kansa albashi ne, sai kuma ya zana ma kansa Dala miliyan 10, sannan kuma ka rika ba shi Dala miliyan 10 din a matsayin albashi, to zai rika karban wannan albashin da hannun hagu ne, na daman sa kuma na satan kudi a wani gurin. Amma mu mun yi matukar sa’a kwarai da gaske, manyan Manajojinmu na da kirki ainun. Kana kuma da yake muna fadada harkokin kasuwancinmu, shi ya sa muke taka-tsantsan wajen daukar mutane aiki. Amma ina tunanin cewa ci gabanmu ma zai rage dukkan wadannan matsaloli, domin su ma ma’aikatan za su zama suna da hannun jari a kamfanin. Zan iya ba mutum hannun jarin Naira miliyan 5, wanda kuma a cikin shekaru 5 zai ninka ya zama Naira miliyan 100. Don in ka dubi wannan adadin jarin da kake da shi a kamfanin, to ba za ka so yin abin da zai saba ma ka’idodin tafiyar da kamfanin ba. In kuma mutum ya yi na kama shi, sannan kuma na kore shi daga aiki, to zai rasa albashinsa na kamar tsawon shekaru 5 zuwa 6. Sannan kuma ina jin cewa bai wa Manaja damar zama wani bangae ne shi ma na kamfanin, hanya ce ta dakatar da akasrin irin wadannan abubuwa.
Har ila yau kuma kamfaninmu ya kunshi ’yan Nijeriya da ma ’yan kasashen waje. Dalili kuwa shi ne muna tafiyar da harkokinmu ne a wasu fagagen da har yanzu ba mu samu kwarewar da za a yi amfani da ita wajen gudanar da irin wadannan maka-makan kamfanoni ba. Saboda haka, a zahiri kana da bukatar taimako daga kasashen ketare ta fuskacin kwarewar aiki. Wannan kuma ba wani abu bane boyayye. A zahiri ma za ka iya dauko hazikan mutane daga kasashen waje don su zo su horar da ma’aikata ’yan Nijeriya. Sannan kuma, a yadda muke tafiya a yanzu, yana da wahala ga wani Manaja na kwarai ya bar kamfaninmu, saboda zai yi hasara ce mai yawa. Domin wasu daga cikin Jami’anmu ne ma suka samar mana da jarin da muke da shi a kamfaninmu na sarrafa sukari. Da hakan kuma sun samu kudade masu yawa. Kamfanin sarrafa simintin da za mu yi nan gaba kuma, zai zama wani abu ne na daban. Misali, in zan ba ka kowane hannun jari a kan Naira 10 ne a kamfanin fulawata, a matsayinka na ma’aikacina, to a kamfanin simintina kuma zan ba ka hannun jarin ne a dai kan Naira 10 din, amma za ka biya ni ne cikin shekaru 5. Amma in ka bar aiki da ni kafin shekaru 5 din, to za ka yi hasarar hannayen jarinka ne. Don haka wadannan abubuwa na daga cikin matakan rike ma’aikaci, sannan kuma a lokaci guda shi ma mai ruwa da tsaki ne, kana kuma abokin tafiya. Saboda haka ba wai mutum zai ta zama a ma’akaci bane kawai ba tare da shi ma yana da ruwa da tsaki a harkar ba.
A matsayinmu na kamfani kuma, muna da tsarin gudanarwa da kuma salon kasuwancinmu. Salonmu mai saukin gaske ne. Sai dai kuma fa aiki ne haikan ba kama hannun yaro.
BAMBANCI NA DA YARANA
Gudanar da kamfani a Nijeriya, ba shakka wani abu ne da ke da kalubaloli masu yawa. Sannan kuma Nijeriya guri ne da ake bambancewa a tsakanin manyan mutane da kuma yaransu. Guri ne da ake bambance Jami’in gudanarwa na gari da mummuna. Wasu mutanen na cewa Nijeriya guri ne da ke da wahalar aiki, to amma gaskiyar magana ita ce cewa babu wani kuma da ke da sauki. Ko’ina ma akwai wahalar, sai dai yana danganta ne da adadin wahalar da ka sha. Nijeriya kam, e, tana da wahalar, amma kuma har ila yau, guri ne da za ka so zuba jarinka a nan. Don a hakika ba daga zuwanka ne kawai za ka kama harkoki ba, ba kuma kawai za ka farka daga barcinka na safe wajen karfe 10 bane ka tafi ofis, karfe biyu kuma na yi ka tashi ba. Wannan kam ba hanyar tafiyar da kasuwanci bace. Don kuwa in da kasar ba wahala, to mun ga jama’a da dama na ta hakilon yin abubuwan da mu ma muke yi. Amma ni kam na yi imani da cewa Nijeriya kasa ce da fursoshin kasuwanci mafiya inganci a duniya. Wasu za su ji maganata tamkar hauka ce, amma dai na’am, maganganu ne na kwarai. Hanyoyin kasuwanci na nan birjik.
Sannan kuma mutane za su sami kudi da su a nan Nijeriyar. Na san kam akwai kalubaloli da yawa, amma in dai kai ba ka iya gudanarwa ba, sai ka nemi inda ba kalubalolin da yawa. Alal misali, kasa kamar Switzerland na daukar abin da kake bukata, ba ’yan fashi da makami, ba komai. Amma kuma ribar nawa za ka ci in kana kasuwanci a can? Wace ribar za ka ci a kasar Switzerland din?
ABIN DA NAKE HANGE
Hangena da kuma tunanina shi ne kafa kasurgumin kamfanin sarrafe-sarrafen da babu irinsa a duk Afirka. Sannan kuma muna tunanin cimma wannan burin nan da shekaru 10 ne masu zuwa. In muka yi haka za mu zama kamfanin da zai rika samun ribar Dala biliyan 15 a kowace shekara. Wannan kuma ina jin cewa ita ce karamar ribar da za mu samu. Insha Allahu kuma za mu cimma wannan burin. Na san cewa mutane za su ce kai, hauka dai kuke yi, amma ba shakka za mu kai ga wannan matsayi. Lokacin ma da muka soma cewa sai mun zama makeken kamfani nan ba da wata jimawa ba, a hakika mutane sun kasa amanna da cewa lallai za mu kai ga hakan. Wannan ne ma ya kawo surutai a ko’ina, saboda rashin sanin irin aiki tukurun da muka yi. Su sun zaci cewa za mu yi tsalle daya ne kawai mu kai inda muka kai a yau. Don a Nijeriya, da an ga kana damawa yadda ka so, to mutane za su yi maganganu iri-iri. Za ka ji suna cewa: Yana da hadaka da wane; su wane da wane ma ya hada gwiwa da su. To mu, in ma mun hada gwiwa da wani, to sune kawai mutanen da suka zuba jarukansu a kamfaninmu ta hanyar kasuwar hannun jari. Don tun zamanin Shagari ma muke da harkokin kasuwanci da yawa. Ina son kuma in ji wanda zai ce ai tsohon Shugaba Shagari ma na da hadaka da ni. Tun daga zamanin gwamnatin Shagari da ta Buhari ma kamfanoninmu ke murza zarensu yadda suke so. Wannan kuma ba zai sa ka ce, ai Buhari ma abokin harkar kasuwancinmu bane. A zamanin gwamnatin Babangida ma, mun ja saniyarmu da abawa. Na’am, Babangida abokinmu ne, amma fa ba shi da wata hadakar kasuwanci da mu. Haka kuma lamarin ya kasance a zamanin Abacha ma. A zamanin Abdussalam Abubakar ma duk kanwar ja ce, na zama ina da alaka da shi ta kut-da-kut, don mun ma yi galibin manyan ayyukan kamfaninmu a zamaninsa ne. Don a zamanin gwamnatinsa ne ma muka muka gina akasarin cibiyoyinmu a tashar jirgin ruwa. Amma ban ma taba zuwa gidansa ba.
BABU KALMAR FADUWA A KAMUS DIN MU
Mun nuna ma ’yan Nijeriya cewa irin abin da za mu iya yi ta fuskacin samar da siminti. Don a Obajana kawai, mun narkar da Dala biliyan daya. Menene ya sa muka narkar da Dala biliyan dayar nan a gina wannan masana’anta kawai? An jarraba mu ne kuma mun ci jarrabawar. Don mun yi makamacin haka a kamfanin siminti na Binuwe. Shi kamafanin sarrafa siminti na Binuwe, kashi 60 ne kawai cikin 100 in aka kwatanta da na Obajana. Misali a nan, lokacin da muka sayi kamfanin siminti na Binuwe, a sakwarkwace muka same shi. Saboda mun dauki watanni 43 muna ta gwagwarmayar neman sayen sa. Da muaka saya kuma, lokacin da muka shiga cikin sa, sai muka tarar da cewa ya riga ya zama wani abin Allah Ya kyauta, yana fama da katutun bashin Naira biliyan 6 da digo 5. Amma yanzu da muka shiga kamfanin, mun narka masa kudade masu dimbin yawa, inda yanzu zai dawo kamar sabo fil. Ko gwamnatin jihar Binuwe ma da ta yi ta gwagwarmaya da mu kan sayen kamfanin, jarinta a cikin sa bai wuce na Naira biliyan 10 ba kacal. Wace jiha ce kuma daga cikin jihohin arewa da ke da jarin da ya kai na Naira biliyan 10 ko da ma a ina ne? Ba ko daya! Saboda haka wannan shi ne sauyin da ke akwai. Wannan kuma shi ne irin abin da muke fuskanta a sayen matatun mai da muka yi. Don cewa muke yi ma gwamnati ba ta da ruwa da tsaki a harkar tafiyar da matatun mai. Don tana da jarin da bai shige kashi 49 ba ne cikin 100, yayin da mu kuma muke da kashi 51 cikin 100. lokacin da muka gyara wadannan matatun man kuma, suka fara aiki ka’in da na’in, to za mu gayyaci ’yan Nijeriya da kansu kowa ya zo ya sayi hannun jari a cikin su. Wala’alla mu samu mutane kamar dubu dari uku da za mu sayar musu da hannayen jari a cikin matatun man. In kuma kamfanin ya fara aiki gadan-gadan, za ku dandani romon hakan, jama’a za su zuba makudan kudade a cikin aljufansu. Don hakan ne ya fi da a ce an rufe matatun man. Kodayake wasu mutane na da tunanin cewa wai manufata ita ce in sayi matatun man in rufe su su daina aiki, don ci gaba da karfafa gwiwar shigo da man fetur da kuma gas daga kasashen waje. To me zai sa a yi hakan? Wane muradi kenan za mu kai gare shi in muka yi hakan? Mu ba mu a cikin harkar shigo da mai, ba ma shigo da man fetur ko wani abu daga kamfanin mai na kasa, NNPC a takaice. Kuna jin cewa za mu je mu ce da bankunanmu su taimake mu da Dala miliyan dari 8 mu zuba su a matatun man, sai kuma mu kulle gurin mu bar shi ba ya aiki? Mu ba haka muke ba. Mu ba wawaye bane. Kuma mu ba irin wannan kamfanin bane. Mu falsafarmu game da harkar kasuwanci ita ce cewa ba mu da kalmar “faduwa” a cikin kamus din mu. Harkar kasuwanci daya rak ne muka taba yi a baya da muka fadi. Shi ma kuma ba yin kanmu bane. Wannan harkar kuwa ita ce wacce muka yi na shigo da kayayyakin masaku. Abin da ya sa muka sami faduwa kuma shi matsala ce da ta shafi kasa baki daya na simogar irin wadannan kayayyaki daga kasahen Sin, wato Chaina, da kuma Indiya. Sannan kuma ba wanda zai iya nasara a wannan gasar. Ko wadanda suka dafe ma wannan harkar ma a yanzu hasarar kudade kawai suke ta tafkawa. Mu kuwa harkokin kasuwancinmu ne ke tafiyar da kansu, in ma ba ka samu kudi ba, to za ka sami mafita. Wannan kuma ya sa muka janye daga wannan harkar. Ita ce kuma bangare daya rak da muka taba samun faduwa. In banda wannan kuma ba mu taba yin wata harkar kasuwancin da muka fadi ba. Don ma muna addu’a kan kada mu sake yin wata harkar da za mu fadi.
A wannan harkar kasuwancin gudanar da matatun man kuma, ba ma jin cewa za mu fadi, za mu maido da wadannan matatun man su rika aiki haikan. Ba ma wai za mu sa matatun su yi aiki bane kawai, a’a, za mu sa mai ya wadata ne; ba kuma wadatuwar man bane kawai za mu kawo, har ma zai yi araha ne. ’Yan Nijeriya ba za su sake rayuwa cikin halin dar-dar din karin farashin man fetur da gas ba. Abin da ya sa ’yan Nijeriya ke sayen mai da tsada kuwa shi ne cewa suna biyan farashin gazawar da matatun man suka yi ne, da kuma barnar da ake yi a kamfanin mai na kasa NNPC. In da kuma NNPC ba ta gaza ba, da sai ta rika samar da mai kamar yadda kamfanin mai na Indiya ke yi. Saboda haka muna ta sayen cuwa-cuwa da barnar da ake yi a NNPC ne kawai. Harkalla da cuwa-cuwa sun ma kamfanin katutu. Wannan kuma ba ya nufin cewa ina zargin wani ne. In na ce cuwa-cuwa a nan, ina nufin cewa jirgin mai zai zo daga waje, amma sai ya yi kwanaki kamar 20 sannan a sallame shi. To wa zai biya kudin wannan jinkiri? Mai saya don ya yi amfani da shi? In kuma ba shi zai biya ba, to gwamnati ce za ta biya. Amma yanzu, za a samu mutanen da za su tafi NNPC kai tsaye su karbi kasonsu na mai. Hatta ma wanda bai san bihim ba zai iya zuwa a ba shi mai a NNPC, ba kuma amfani zai yi da shi ba, zai sayar ne abin sa. Wanda ya saya din kuma zai sayar ma wani ne shi ma, wancan kuma ya sayar ma wancan, daga irin wannan hawa-hawan ne sai ka ga lamurran sun ricabe, wanda kuma dole a kawo karshen hakan. Amma yanzu sauyi ya samu, inda za a rika sayen mai a farashinsa da ya dace. Don in aka kasuwantar da abu, to fa babu wani sauran karkasawa. Ni in ina samar da man, to ba zancen karkasa wani abu.
WANDA YA FI KOWA DUKIYA A DUK AFRIKA
Ni ba zan kira kaina mutumnin da ya fi kowa dukiya ba a Afrika. Ba kuma zan sa mujallar FORBES ta ce haka ba, amma dai na ga sun ce wai Opra Winfrey ce ta fi kowa dukiya a tsakanin dukkanin bakaken fatar duniya, saboda tana da Dala biliyan 1 da digo 5. Amma dai ina jin cewa na fi ta nesa, nesa ba kusa ba. Amma kuma wani abu game da Afrika shi ne, cewa zan tsaya in jira mujallar FORBES ta sake fitar da jimlarta tukun. A nan ne, komai zai bayyana a fili balo-balo a karshen shekara. Na san za su buga mujallar a watan Fabrairu. Kenan sai mu zuba ido mu gani.
WADANDA NAKE KOYI DA SU A KASUWANCI
Ina son yadda wasu kamfanonin kasauwancin Indiya ke tafiyar da harkokinsu. Wadannan kamfanoni kuwa sune Reliance Group da Tatas. Ina ma jin cewa muna da abubuwa da dama iri daya da kamfanin Reliance Group, saboda su ma suna fadada tunani, don haka ne kuma suke aiwatar da manyan ayyuka. Alal misali, sun shiga cikin harkar kasuwancin manyan shagunan sayar da kayayyakin masarufi (supermarkets). Sannan kuma gina matatar man da ke tace ganga dubu dari shida da sittin a kullum. Wannan fa matatar mai kwaya daya ce rak, kana kuma ita ce ma mafi girma a duk duniya, saboda sun yi ta kara mata girma. To irin wadannan abubuwan ne mu ma muke magana a kai. A shekaru 10 da suka gabata wannan matatar man bai yi girman haka ba alal hakika. Sannan ma a shekarun saba’inoni, shi mai wannan kamfanin, mahaifinsu ya kasance a matsayin mai sayar da mai ne a wani gidan mai, da haka ya fara. Shi ne mai zuba wa motoci mai in sun je sha. Kuma ya kasance yana rayuwa ne a wani dan karamin gida tare da iyalinsa, amma kuma tunaninsa shi ne wata rana ya gina matatar mai. Amma ni kuma tunanina zai fi tabbata a zahiri cikin hanzari fiye da nasa. Sai dai abu daya ne kawai, shi ma yana taka tasa rawar ce a manyan harkoki kasuwanci.
Mu kuma a namu bangaren, kamfanin Dangote na kara habaka. Don irin rawar da muke takawa yau, ya wuce na fagen kafa masana’antun samar da kayan abinci. Domin kafa masana’antun samar da kayan abinci ba ya cin kudade da yawa. Mu kuma wannan fagen yanzu ya yi mana ma kada. Don haka ya kamata mu hari na gaba da shi, kamar shiga cikin harkar mai, iskar gas, da kuma wayar sadarwa; inda za mu bukaci zuba jarin da bai gaza na Dala biliyan 3, 4, zuwa 5 ba. In kuma lamurra ba su sauya ba, to muna sa ran cewa harkar zuba jarinmu a fannoni daban-daban cikin shakaru 4 masu zuwa, ba za ta gaza ta Dala biliyan 10 ba. Na san cewa wani zai ce, in ma kuka sa kashi 10 cikin 100 kuma ta ina ne za ku samu Dala biliyan 3 kuma? To muna dai ci gaba da tarawa ne, sannan kuma ma mun tara akasarin kudin da muke bukata. Sannan kuma za mu cimma wannan buri. In ma kuma an samu wani sauyi a wannnan muhallin da muke ciki, to mu dai za mu ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinmu. Don mu ba kanfanin da gwamnati ta mallaka bane. Don mutane har yanzu suna gudanar da harkokin kasuwancinsu a guraren da ake fama da rikice-rikice kamar su Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango. A kashin gaskiya ma, Kwango na daga cikin kasashe mafiya muhimmanci da mutum zai iya zuba jari. A lokacin yakin Laberiya ma mutane sun ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu a can. A watannin shida da suka wuce ma, wani abokina ya je Kwaddi Buwa ya kafa kamfanin sarrafa garin fulawa a can. Amma kuma dukkanin wadannan kasashe Nijeriya ta fi su fursoshin kasuwanci na kwarai, saboda mu ba ma cikin halin yaki, duk da cewa akwai matsalolin yankin Neja Delta, amma dai wannan wata matsala ce da ya kamata mu fuskance kai tsaye. Sannan kuma ina jin cewa wannan gwamnatin ta Shugaba ’Yar’aduwa na ta kokarin kawo karshen matsalar. Wannan ya sa nake da karfin gwiwa kan ci gaba da wanzuwar Nijeriya a matsayin dunkulalliyar kasa. Amma abin da nake tsoro kawai shi ne rikicin yankin Neja Delta. Don da zaran a ce mun warware wannan matsalar, sannan kuma muka sami bakin zaren warware matsalar rashin wadatacciyar wutar lantarki, kana kuma muka dubi lamarin yaki da talauci da idon basira, to mun gama da wasu daga jiga-jigan matsalolin da suka sha mana kai. Saboda ina da amannan cewa ba a yankin Neja-Delta ne kawai muke da matsala ba; domin ko da mun kawar da matsalar yankin Neja-Delta din, to Neja-Delta ta gaba za ta bayyana mana a Arewa, inda matsalar talauci ke da girma ainun. Saboda haka akwai bukatar a sake duba manufofinmu na aikin gona ta yadda za a bunkasa shi. Sannan kuma mu tabbatar da cewa mun mai da hankali wajen kakkafa masana’antu, don ba zai yiwu ba a kasa a samu wani gurin da mutane za su yi ta zama a inuwar bishiya tun daga safiya har yamma, alhali kuma gurin na da albarkar yawan jama’a.
LABARINA KAN SAYAR DA KAMFANONIN GWAMNATI, DA CUWA-CUWAR DA AKE YI A NNPC
Gwamnati ba ta kashe Dala biliyan 1 da digo 1 ba don gyara matatun mai, kamar yadda wasu jaridu suka fada. Ni na san wannan hakikanin gaskiyar. Jaridun kuma suna nan. A shekaru 3 da suka wuce dai gwamnati ta ba kamfanin mai na kasa, NNPC a takaice, Dala miliyan 700 don farfado da matatun mai. Amma ba a yi aiki da kudin a yadda ya dace ba. In ma kuma an yi din, to har yanzu dai matatun ba sa aiki. Kuma ma ba su da wata kima. Na farko kenan. Na biyu kuma, ba wai kawai mun tashi mun kai kanmu bane muka ce: “To, nawa za mu ba ki?” ba. An yi gasa ne da kuma bin wasu matakai. Kamfanin Credit Swiss sun yi iya nasu tantancewar, wanda kuma ko kusa bai ma kai abin da muka biya ba. NNPC ma sun yi nasu, wanda kuma ya zama kasa da namu da kamar kashi 40 cikin 100 na farashin da muka sai matatun. Daga nan kuma sai BNP Paribas ta shigo ta yi iyakacin nata tayin, da ta gaza kuma sai ta gayyaci BTE da ta zo ta yi nata, amma duk guda biyun na kasa da abin da mu muka biya. Wannan kuma duk ya wakana ne mako daya kacal kafin mu sayi matatun. Kodayake kafin mu mu je kamfanoni biyu ma sun yi nasu tayin; na farko shi ne Petro Plas, sai kuma Sahara Energy, inda su biyun suka yi hadaka, amma ina! Su sun taya ne a kan Dala miliyan 300 su biyun. Amma kuma fa sun ma kasa bayar da kudin shigan biya. Saboda haka ne ma aka ce ba su cancanta ba. Kamfanin mai na Oando ma ya zo ya taya Dala miliyan 200, sai aka ce ya kawo rabin kudin, maimakon ya ba da Dala miliyan 100 kuma, sai ya bayar da Dala miliyan 80. Su ma dai aka ce ba su cancanci sayen matatun man ba. Mu da muka taya Dala miliyan 200, sai aka ce mu kawo rabin kudin a matsayin shigan biya, nan fa muka cake Dala miliyan 100. Kai, sai aka ce da mu wai ko ma mu sake sabon tayi a wani sabon farashin. Amma mu da yake mun san irin sarkakiyar da ke tare da wadannan matatu na cewa akwai mutane da yawa da ke zaman cin kudade ta hanyarsu, kama daga masu sana’ar shigo da mai daga kasashen waje, har zuwa kuma wadanda ke kamfanin mai na kasa, NNPC, da ke samun rashawa ta hanyar bayar da kason mai; sai muka lakanci cewa ana fa da dandazon mutane da ke karbar rabon wannan mai din ko wancan. Sakamakon haka ana iya samun wani ya hau karagar mulki ya yi yaki da mu. Da muka gano haka, sai ba mu nuna damuwa ba kan ko nawa ne aka yi wa matatatun man kimar kudi. Sai muka ce bari mu ci gaba kawai, a nan sai muka fara da matatar mai ta Fatakwal, inda muka yarda za mu bayar da Dala biliyan 1 da digo 1. Nawa ne ma gwamnati ta kashe a 1989 ne wajen gina wadannan matatun? Sannan kuma ma an samu koma baya, bayan gina wadannan da shekaru, sannan wadannan matatun man sun sakwarkwace, sannan kuma ba za a dawo ma da kudin da ka bayar ba lokacin tayin nan, sai kawai muka biya farashin dala biliyan 1 da digo dayan nan, sannan kuma Dala miliyan 561 da muka bayar kan matatar mai ta Fatakwal, shi ne kashi 51 cikin 100 daga cikin Dala biliyan 1 da digo 1 din can. Ka ga kenan ba wai mun sayi matatun man bane gaba dayan su. Har yanzu gwamnati na da kashi 49 cikin 100 na jarinsu. Mun dai sayi kashi 51 ne kawai. Sannan kuma kashi 51 cikin 100 na Dala biliyan 1 da digo 1, shi ne Dala miliyan 561.
Game da matatar mai ta Kaduna kuma, Sinawa, wadanda ’yan Nijeriya ba su cika damuwa da su ba, in ana maganar fadawar matatar man hannun ’yan kasasahen waje ne, an ba su matsayin gigga a harkar mai. A ran da suka kattaba hannu kan yarjejeniyar samar da mai ta hanyar hadaka, a ran nan ne suka ce: “to mu ba fa tayi muke yi ba, sai dai kawai mu kattaba hannu don karbar mai.” To wadannan mutane, bayan sun kattaba hannu kan yarjejeniyar karbar mai, sai suka taya matatar man a kan kudi Dala miliyan 102 kacal. Suka kuma kafe kan cewa ba fa za su kara kwandala ba a kan abin da suka taya din nan. Mu kuma sai muka ce, to madalla, a maimakon mu bar gurin ya tsaya ya rube, sai muka rubuta takarda muka nuna muradinmu na sake tayawa. Farashin da su Sinawa suka taya matatar man kuma yana kasa kwarai da abin da aka yanke. Mu kuma sai muka bayar da kashi 60 cikin 100 na abin da Sinawa suka taya. Wato muka saya Dala miliyan 160 duk da kalubalen da muka yi ta fuskanta. Kuma ina jin wadannan matatun man ne aka tabb ba kamfanonin mai irin su SHELL, CHEVRON da kuma TEXACO, amma suka ce ba sa so, don su ba za su gudanar da abin da ba zai haifar musu da komai ba. Amma mu da muka biya sama da Naira biliyan 100 yau, mutane sai hayagaga suke ta yi. Saboda haka ina ganin ya kamata mutane su yi wannan hayagagar tasu ne a kan kamfanin sarrafa sinadaran man fetur na Eleme. Don shi ne ma kamfanin da gwamnati ta kashe masa Dala biliyan 1 da digo 5, amma kuma ta sayar da shi ga wani kamfanin kasar wajen da bai ma taba ziyartar kasar nan ba, a kan kudi Dala miliyan 200 kacal. Abin lura a nan shi ne cewa, da yake su kamfanin kasar waje ne, ba wai kashi 51 cikin 100 na jarin kamfanin suka saya ba, kashi 71 ne suka saya. Amma kuma ma yaba musu ake yi. Amma mu a matsayin mu na DANGOTE mun yi hasara ne a wannan kamfanin don mun kashe sama da Dala miliyan 5 zuwa 7 wajen gayyato kwararru daga kasashen waje don su zo su kalkale bincike da kuma kalailaice komai, amma ba a sayar mana ba, mun dai yi hasarar kudinmu kenan, amma ’yan Nijeriya ba su ce komai ba da aka sayar ma wani kamfanin kasar waje.
Batu na uku kuma shi ne sayar da kamfanin mulmula karafa na Ajaokuta. Wannan kamfanin kusan ya tsunduma Nijeriya cikin bashi iya wuya. Don gwamnatin Nijeriya ta narka kudin da bai gaza Dala biliyan 4 da digo 4 ba. Sannan kuma duk wadannan kamfanonin kasashen wajen ba wanda ya kawo kwandalarsa a cikin kasar nan, kudin da suka sayi kamfanin ma da shi sun ara ne daga bankunan cikin gida na kasar nan. Amma kuma dai wadannan kamfanonin ne dai suka sayi wannan kamfani a wani kudin da bai kai cikin cokali ba na Dala miliyan 300 kawai. Wato kashi 60 cikin 100 kenan na jarin kamfanin da gwamnati ta kashe ma Dala biliyan 4 da digo 4. Amma ’yan Nijeriya sai shiru suka yi da bakin su, amma kuma a lokaci guda suna korafi a kan namu. Watakila saboda mutane ba su da sha’awa a kan harkar masana’antun sarrafa karafa ne shi ya sa. Alal misali, kamfanin mulmula karafa na Delta, gwamnati ta kashe masa Dala biliyan 1 da digo 45, sannan kuma ta sake yi masa gyara a kan Dala miliyan 45, amma kuma ta sayar da shi a kan Dala miliyan 30 kacal, shi ma kuma za a biya ta cikin shekaru uku masu zuwa. Sai dai fa ba wai ni ma ina korafi a kan yadda aka sayar da wadannan masana’antu bane, sannan kuma ba ina korafi ga farashin da aka sayar da su bane kuma. Abin da nake cewa shi ne, in har wani zai yi korafi ma, to ya yi korafinsa kan yadda ’yan kasashen waje ke mallake mana kadarori.
A kamfanin sarrafa farin karfen goran ruwa na ALSCON kuma, nan ma gwamnati ta kashe Dala biliyan 3 da digo 4. Amma wasu Rashawan da ba su ma taba zuwa Nijeriya ba sun sayi kamfanin a kan Dala miliyan 200 kawai, sannan kuma bisa sharadin cewa sai ran da gwamnati ta yashe kogin kwara tukun sannan za su biya kudin. Shi kuma abin da za a kashe wajen yashe kogin shi ne Dala miliyan 260. Saboda haka a nan, ka dubi dai yadda sai da gwamnati ta sadaukar da Dala miliyan 60 dinta don ta samu ta rabu da kamfanin ALSCON. Domin in ba haka ba, gurin zai ci gaba da sakwarkwacewa, sannan kuma mutane za su dinga kwankwance kayan masana’antar da sata. Saboda haka gwamnati ta ce, “bai kamata mu ci gaba da narka kudade a gun ba. A maimakon haka ma, gara dai mu cefanar da shi kawai ko da a wani dan kudin da bai taka kara ya karya bane.”
Bisa ga gogayyar da na samu a kasashen ketare, dangane da mayar kamfanonin gwamnati masu zaman kansu, za mu iya cewa mai so ya saya ko da a Dala daya ma, da haka sai a ga mutum ya mallaki wani kamfani. Domin in ka mallaki wani kamfani a matsayinka na mai zaman kanka, to za ka tafiyar da shi yadda ya dace, mutane kuma za su samu hanyar samun abin rayuwa ta wannan kamfanin, don zai samar da guraben ayyukan yi.
Dangane da batun matatar man fetur kuma, da ma mun kattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin mu da gwamnati ta kafa wata matatar mai a Lagos, wacce kuma za ta rika samar da mai ninki biyun abin da na Fatakwal da Kaduna ke samarwa su biyun. Wannan yarjejeniya kuma tsakanin mu da gwamnatin tarayya tana nan a rubuce, za kuma mu aiwatar da ita.
SASANTAWA TSAKANIN GWAMNATI DA KUNGIYAR KWADAGO TA KASA, NLC
Wannan batu kuma ya taso ne a daidai lokacin da ake zaman sasantawa tsakanin gwamnati da kungiyar Kwadago kan batun karin fashin man fetur. Ita NLC din ce da kanta ta fara shigo da batun kan matatun mai. Lokacin da muka zauna da su ne kuma suka gamsu cewa sun amince a shigo da batu kan matatun mai. Wani abu kuma zai ba ka mamaki da kuma kaduwa shi ne cewa bangaren gwamnati ne ya fi rakadin shigar da batu kan matatun mai a wajen sasantawar, amma kuma sune ke dari-darin kin warware lamarin. Saboda suna son da ma batun ya zama wani kakon da za a yi ta kiki-kaka a kai, wanda daga bisani gwamnati za ta fusata ma ta ce ta fasa sayar da matatun man. Saboda haka sai harkallar da ake yi a gun ta ci gaba kamar yadda aka saba, musamman ma ga wadanda suka dogara da wannan cuwa-cuwar. Amma bisa sa’a, sai ba a kai ga hakan ba.
|