Jaridar Bunkasa Kasuwanci da Siyasa
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
DILLALIYAR KANO

Mu iyakacinmu ba da shawara

In ji Alhaji Bashir Yusuf Burum-Burum

Wannan hira ce da jaridar DILLALIYA ta yi da dan majalisar tarayya mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa, Alhaji Bashir Yusuf Burum-Burum. Dan majalisa ne da yake tare da jam'arsa, don kuwa abin sha'awa, mun sami dan majalisar ne a garinsa na Burum-Burum a cikin jama'arsa. Ga yadda hirar ta kasance:

'YAN MAJALISA SUNA IYA KOKARINSU

Jama'a suna zargin 'yan majalisu da rashin taka wata rawa ta musamman dangane da irin abubuwan da suke faruwa kusan a kasa baki daya. Gaskiyar magana ni a nan ba wai don ina dan majalisa ba, a matsayina ma kurum na Basiru, na san majalisa fisabililLahi abin duk da za a gaya wa Shugaban kasa don a kyautata wa mutane ko don kyautatuwar jin dadin jama'ar kasa, majalisa tana yi.

Mu iyakacinmu fa ba da shawara, gudanar da abubuwa, majalisar zartarwa ta kasa ita ya kamata ta gudanar. Don ba mu da hakkin dauko aikin hanya ko daga Kaduna zuwa Kano, ba mu da wannan hurumin. Muna da hurumin dai ba da shawara, na abin da ya kamata a yi, aiwatarwa ba namu bane. Ka san harka ta mutum a siyasa, kai za ka goya mutum ka rene shi, sai ka taras shi ne yake kokarin ya tura ka rana. Ballantana mutumin da haduwa kuka yi, wani soja ne, wani dan sanda, wani malamin makaranta, ka ga a nan dole ra'ayi ya sha bamban. Fisabilillahi muna ba Shugaban kasa shawara, sanin halin kunci da ake ciki da talauci, rashin aikin yi, wanda hakan yake jawo fashi, abubuwan ma yanzu ya dada tabarbarewa, wannan yana bata mana rai. Na san nan gaba abubuwa za su kyautatu.

DA ANPP CE TAKE DA GWAMNATIN TARAYYA, DA BA WATA JAM'IYYA DA ZA TA SHURA

Ba gaskiya bane cewa don mun fito daga jam'iyya daya da Shugaban kasa, muke mara masa. Duk abin da zai zama alheri mu masu son mu ga jama'a sun samu ne. Kuma tsakani da Allah, ni a inda nake ganin abokan adawarmu, da su Allah Ya bai wa wannan matsayin, wallahi ba wanda zai shura. Wannan zargi da suke, to mene ne aka zo da shi wanda zai amfani kasa ko talakawan kasa na arewa, kudu da tsakiya, wanda aka kawo shi majalisa ba mu mara masa ba? In sun kawo magana ko ta sayen jirgi na Shugaban kasa, in Shugaban kasar nan ya sayo jirgin nan, ai ba shi zai amfani da shi ba, ba kuma nasa bane, in shi ne Shugaban kasa yanzu, 2007 wa ya sani? Sai Allah! Za ta iya yiwuwa daga wata jam'iyya ne, tunda dai mulki na Allah ne. Ba wai Shugaban kasa zai saya ya tafi da shi Otta, gonarsa bane, ko ya mai da shi jirginsa in ya sauka, ya tafi da shi. Ai babban abin farin ciki ne ma a wurin gwamnati a ce ta sai abubuwan da za su zama 'asset', wanda ko ba ka nan in aka duba baya za a ce ai a zamanin wannan aka yi kaza, aka yi kaza. Zargi suna yi ne don ganin ba su bane. A tafiyar da ake ana yi masu adalci. Misali kamar irin abubuwan da aka yi a zaben Kananan Hukumomi a Kano. Mu a PDP da mun san ba za a yi mana adalci ba, ba za mu shiga zaben ba, kamar yadda 'yan uwanmu na PDP a Sakkwato suka yi, kamar yadda suka yi a Legas da Zamfara, duk jam'iyyunmu ba su shiga zabe ba, domin sun san ba za a yi masu adalci ba. Da mun san haka ne, a nan Kano, ba a kawo mana Allah a baki ba, da ba mu shiga zabe ba, don an ci zarafin mutane, an ci mutuncinsu kurum, an zo ana fadan karya, wanda ba haka ya kamata a yi ba.

BA WATA JAM'IYYA DA TA YI ADALCI GA 'YAR UWARTA A ZABEN KANANAN HUKUMOMI

Ba wata jam'iyya a tsakani da Allah da ta yi adalci ga 'yar uwarta, dangane da zaben Kananan Hukumomi, don ni kafin na zo majalisa na yi shugabancin Karamar Hukuma sau biyu, amma na san mutane ne suke zabe na, saboda Allah Ya ba ni. Inda yanzu kowace jam'iyya, ban ce ANPP kawai ba, yadda AD ta yi a Legas haka ANPP da PDP suka yi, abin ya zama kowa tunaninsa. Sai wanda ya fito daga jam'iyyarsa ne zai zama wani abu, wanda kuma in an duba, mulki na Karamar Hukuma, shi ne ya fi dacewa mutane su zabi abin da suke so. Ya dace a bai wa kowa dama, don duk 'yan kasa ne mu. In da an yi adalci, duk wanda ya san an yi zabe tsakani da Allah, faduwa ya yi ba zai damu ba, don ya san Allah bai ba shi ba, amma abu mara dadi shi ne a ce an yi fin karfi.

WANNAN YANAYI BA ZAI DORAR DA DIMOKURADIYYA BA

Irin wannan yanayi ba zai dorar da mulkin dimokuradiyya ba, kuma ba zai haifar da da mai ido ba. Ya kamata a yi gyara, a rusa Hukumar zabe ta jiha din nan. A yi ta kasa, shi ne zai zama alheri. Yanzu misali kamar a Abuja, a Abuja Kananan hukumomi shida ne, amma da aka yi zabe ba magudi, uku da uku aka yi. Ko ba ka kaunar Allah ka san an kwatanta gaskiya. Da haka aka yi a jihohi, da zai fi mana alheri.

KOWANE GWAMNA TUNANINSA, JAM'IYYARSA TA SHARE KOWANE MUKAMI

Zaben da ya gabata ana cewa, an tafka magudi a wasu wurare, amma ba a tabbatar da tafka magudi kamar wannan na Kananan Hukumomi ba, don ba maganar PDP ko ANPP, kowane Gwamna tunaninsa kurum jam'iyyarsa ta share duk wani mukami da yake jiharsa. Wane ne ma ba magudin yake ba? In aka ce ba wanda zai kwatanta gaskiya, abubuwa sun baci. Gara komai kankantarta a kwatanta.

MUN SAMAR DA RUWA DA WUTAR LANTARKI

Zamana na majalisa na farko, mun yi abubuwa na samar da ruwa a Tudun Wada da Doguwa. Mun yi yunkuri an gyara gadar Yaryasa da abubuwa da dama. Akwai ayyuka da suka shafi karkara da za a yi.

MU HADA KAI DON TAIMAKA WA AL'UMMA Ina jan hankalin jama'a da yin hakuri da junanmu. Duk wanda yake shugabanci zai iya samun adawa ta ko'ina, kuma duk abin da ka yi komai kyawunsa, a gun wani ba mai kyau bane. Irin wadannan su yi hakuri komai lokaci ne, a hada kai, don taimaka wa al'ummarmu.

Ziyarar Gwamna Turai da Amurka

Bagwai, Tarauni sun yaba

Shugaban Karamar hukumar Bagwai Hon. Yusuf Ahmad Badau, ya bayyana tafiyar da Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau yayi zuwa wasu kasashen Turai da Amurka a kwanakin baya da cewa mabudi ne na ilimi, don kuwa tafiya ce da aka gano hanyoyin ciyar da jiha gaba.

Hon Yusuf Badau ya shaida wa jaridar DILLALIYA cewa, suna da zaton samo hanyoyin inganta al'amuran tafiyar da rayuwar dan Adam, kama daga noma, ilimi, gami da zamantakewa. Ya ce ziyarar an yi ta ne don ganin yadda kasashen suka ci gaba da jin hanyoyin da suka bi suka sami habaka.

Yusuf Badau ya yi nuni da cewa wannan ziyara da Gwamna ya yi, ya je ya dawo lafiya, riba ce babba ga Kananan hukumomi, don zai assasa masu hanyoyin ciyar da su gaba, da dogaron kai.

Sannan ya yi kira ga jama'ar Kano gaba daya su dau wannan ziyara da Gwamna ya kai ya dawo da cewa riba ce. Ya ce 'yan adawa da suke ta korafi a kan ziyarar, duk abin alherin da za a yi, komai kyawunsa, cewa za su yi ba a yi daidai ba. Ya ce za su ci gaba da toshe kunnensu, don kuwa su alheri suka sa a gaba.

Hon. Yusuf Badau ya ce su gwamnatinsu tunaninsu, shi ne dadada wa rayuwar al'ummar Kano. Ya ce abin alfahari shi ne, a wannan tafiya da Gwamna ya yi ta ilmantar da wadanda suke ganin addinin Musulunci da wata fassara ta daban. Shekarau ya sanar da su mene ne addinin da kuma shari'a, sun kuma fahimci hakan.

Hon. Yusuf ya yi addu'a ta fatan samun ci gaba da kira ga jama'a su rika addu'a ga gwamnatin Kano.

Shi kuwa a nasa sashen, mataimakin Shugaban Karamar hukumar Tarauni, Hon. Jalli Abdullahi, ya bayyana cewa, ziyarar da Shekarau ya kai, abin farin ciki ne. Ya ce da yake ziyarar gayyata ce asalinta don wayar da kai, kan matsayin shari'ar Musulunci, ba karamar riba bace. Ya je ya yi jawabai kan mene ne ma shari'ar Musulunci, da amfaninta ga al'umma. Duk inda ya je, sun zauna sun tattauna, sun fahimci juna.

Jalli Abdullahi ya ce duk wani addini da ya yarda da Allah, bai amince da zina, sata, kwace da ayyukan da suka saba ba. Ya ce, "zuwan Malam ya fahimtar da su shari'a da yadda ake yin ta. Baya ga haka kuma, wata riba ce ga Kano ga dangantaka ta kasuwanci. Ya ce ga wadanda ke ganin ziyarar ba ta da amfani, ba su fahimci me ye ma dalilin tafiyar ba. Su bincika, za su tarar alheri ne.

Za mu fadada asibitin Albasu

An bayyana cewa babbar matsalar da ta fi ci wa al'ummar Albasu tuwo a kwarya ita ce matsalolin ruwan sha da harkar lafiya. Wani dan yankin Karamar Hukumar ta Albasu mai suna Alhaji Lamido Idi ne ya shaida wa jaridar DILLALIYA hakan da take zantawa da shi a Albasu.

Alhaji Lamido ya yi nuni da cewa, ta kai idan mutumin Albasu ya sami rashin lafiya, sai an kai ga daukarsa a kai asibitocin makota, ko a Wudil ko Birnin Kudu, kafin ya sami sauki, saboda rashin kayan aiki da likitoci da kuma kuncin asibitin.

Alhaji Lamido Idi ya kara da fadin cewa a yanzu sun san duk wadannan matsaloli suna kusa da karewa, saboda zaben da suka yi wa Alhaji Musa Tahir a matsayin shugabansu na Karamar Hukumar.

Ya ce sabon Shugaban na Albasu mai kwazo ne, wanda ya zo a lokacin da mutane a Albasu suke wani yanayi na cin ruwa, suka sami wanda zai yi masu fito. Ya ce shugaban yana da tsare-tsaren da suka shafi noma, lafiya, ruwan sha, wanda da kyakkyawan fata za a sami kyakkyawan canji a yankin.

Shi kuwa a nasa bangaren, Shugaban Karamar Hukumar na Albasu, Alhaji Musa Tahir Hungu, ya ce suna nan shiri ya yi nisa don gyara asibitin Albasu da fadada shi, da samar da kwararrun likitoci, da samar da magunguna don amfanar Albasu da al'ummarta.

Ya ce batun ruwan sha kuma suna nan suna tuntubar mazabu kan su binciko, duk inda ake da matsalar ruwa take a yankin, a ko'ina cikin lunguna da sakunan yankin don magance rashinsa.

Komawa babban shafinmu                                   Komawa saman wannan shafin