Harkar finafinan Hausa:
Kar a yi fargar jaji
Daga Abdullahi Aliyu Moving image Ltd, Kano
Mai karatu wannan wani bangare ne daga mukalar da marubucinta ya gabatar a wani taro kan finafinan Hausa. Farko-farkonta ya bace mana, amma duk da haka muna ganin akwai abin fahimta sosai a abin da ya yi mana saura. A sha karatu lafiya.
a) Hukuma
Duk halin da harkar fim ta shiga a yanzu walau na ci gaba ko rashinta, dole a dora shi a kan hukuma. Hukuma a wannan mukala, na nufin hukumar tace finafinai ta jihar Kano, domin ita ce wakiliyar gwamnati a cikin harkar. Idan ba a manta ba, an kirkiro wannan hukumar ce bayan da aka dage haramcin da aka sanya wa harkar finafinai a Jihar Kano. Manufar kafa ta kuma shi ne don ta dinga sa ido ta ga cewa lallai finafinan da ake shiryawa sun dace da al'ada da kuma addinin Musulunci. Ainihin tacewar a nan, ita ce a tabbatar da cewa duk fim din da ya saba da wadannan ka'idoji, bai samu shiga kasuwa ba, ko kuma ma a soke shi gaba daya. Ba wai wannan ne kadai aikin hukumar ba, sai dai kawai na takaita ne bisa abin da ya shafi wannan mukala.
Daga cikin 'yan wannan hukuma akwai Malamai (Sheikh Yusuf Gama shi ne Shugabanta), da ma'aikatan gwamnati, da kwararru a kan harkar fim, da wasu daga cikin su kansu masu shirya fim din. A yadda aka tsara wannan hukuma, da wuya fim din da ya saba ka'ida ya kai labari. To amma abin mamaki, a kullum sai ka ga irin wadannan finafinai suna ta shigowa gari, kuma da tambarin hukumar, wanda ke nuna cewa an tace su. A zahirin gaskiya da hukumar na aikinta, to da wuya wasu finafinan, musammam ma dai na Dan Ibro, su samu fitowa. Wani abin takaici ma shi ne yadda hukumar ta kyale ake ta nuna finafinan batsa na wasu kasashen a gidajen talabijin na jihar, musamman ma dai CTV Kano, amma kuma ba ta taba cewa komai ba. Haka ma abin yake a gidajen sinima. Akwai ma wadanda suke kare nuna finafinan wasu kasashen da cewa wai Hausawa ba su fahimtar harshen da ake magana da su a finafinan. Don haka hoto kawai suke gani. Amma na Hausa suna fito da muggan abubuwa ta hanyar amfani da harshen da kowa yake fahimta. Sai dai kuma sun manta da abu daya cewa shi fim ko mutum yana fahimtar harshen da aka yi shi da shi, ko ba ya fahimta, ba zai hana ya dauki wasu munanan dabi'u daga cikinsa ba. Za mu iya ganin gaskiyar haka ta irin askin nan na shedanu da 'ya'yanmu suke yi, da kuma manyan wanduna da rigunan da suke sawa, da kuma yadda suke tafiya a jirkice, da sauransu, wadanda idan dai za mu fadi gaskiya, ba a cikin finafinan Hausa suka gani ba. Wani masanin finafinai, Edison Egbe, ya bayyana cewa kowane irin fim, yana zaman yare ne na gama-gari mai zaman kansa. Wato dai ko da ba a magana a cikinsa, mutum zai fahimci abubuwa da dama, har idan da za ka tambaye shi zai iya gaya maka labarin fim din kamar ya ji abubuwan da aka fada. Wadanda suka dade suna kallon finafinan Indiya za su iya tantance wannan batu nawa.
Ni abin da nake ganin ya dace hukumar tace finafinai ta yi, wanda kuma nake ganin lallai da zai rage duk wasu abubuwan ki da ake ta'allaka finafinan Hausa da su, shi ne ya kamata a ce hukumar ta fito da wani shiri kowane wata, ko kuma duk shekara, na zabar wasu daga cikin finafinan da aka shirya, wadanda kuma suka cika ka'idar da ta jibanci addini da al'adar Bahaushe, sai ta ba da wata kyauta ta musamman ga wadanda suka shirya wadannan finafinan da suka dace.
Haka kuma baya ga wannan kyauta da za ta ba su, yana da kyau ta shawarci gwamnati da ta sa a rika nuna wadannan finafinai a gidajen talabijin. Na yi imanin cewa duk wanda ya ga ya samu kyauta saboda ya shirya fim din da ya dace da shari'ar, to akwai kyakkyawan zaton cewa zai kamanta wani kamar wancan. Su ma kuma sauran masu shirya finafinan, za su yi hankoron ganin sun yi finafinan da za su kawo musu ci gaba da kuma zaman lafiya da hukuma da kuma sauran jama'a.
b) Matsayin Malaman addini
Su ma Malaman addinin Musulunci na daga cikin wadanda za a ba wani kaso na laifin jefa finafinan Hausa halin da suke ciki a yanzu. Ya kamata a ce kamar yadda sukan yi wa'azi da ba da fatawa a kan sauran matsaloli na addini da rayuwa, to ya zama suna bayarwa a kan harkokin finafinai. To, a zahiri, abin sam ba haka yake ba. Daga cikin Malamai akwai wadanda ba su taba tsayawa sun kalli wadannan finafinai ba, sai dai kawai wasu su zo su ba su labari cewa an yi kaza da kaza a fim kaza. Alal misali, na taba yi wa Limamin masallacin Tudun Murtala, Malam Abdullahi Pakistan tambaya a kan cewa ana zargin Malamai ba sa kallon wadannan finafinai, amma sukan yi sharhi a kai. Sai ya nuna cewa idan har Malamai suka tsaya kallon wadannan finafinai wadansu za su yi masu mummunar fahimta. Abin tambaya a nan shi ne: Ko zai yiwu mutum ya yi sharhi a kan abin da bai san shi ba? Akwai kuma wani lokaci da kungiyar mata musulmi suka shirya wani taron tattaunawa akan finafinan Hausa. A dandalin wasa na Sani Abacha, inda aka gayyaci Malamai kamar su Sheikh Umar Kabo da Ustaz Bin Usman, da Malam Farouk Chedi, da kuma Shugaban majalisar masu shirya finafinai ta kasa, MOPPAN, Malam Abdulkareem Muhammad. Babban abin da yawancin Malamai masu jawabi suka nuna shi ne, ana tafka kurakurai a harkar finafinan Hausa.
To amma kuma tambayar da Malam Abdulkareem ya yi musu wadda kuma aka kasa amsawa ita ce: Wace irin gudummawa Malamai suka taba bayarwa wajen ganin an tafi da wannan harka daidai? Kusan za a iya cewa finafinan da suka fito daga bangaren masu son gyara ta fuskar addini ba su taka kara sun karya ba (Karbala, Shaheed, Tafarki, Kadaura dss.) Musammam idan aka yi la'akari da yadda ake fitar da sauran finafinai wadanda jigonsu ba addini ba ne.
c) Kwararru
Kamar yadda na nuna a baya, ana yawan zargin masu shirya finafinan bidiyo na yanzu da rashin kwarewa. Wannan gaskiya ce, amma abar tambaya a nan ita ce, wace irin rawa kwararrun suka taka wajen kawo sauyi a harkar? Kuma a zancen da ake yi yanzu, finafinai nawa ne daga cikin dubban da ake da su suka fito daga bangaren kwararru? Finafinai kamar su Alhaki Kuikuyo, da Waiwaye Adon Tafiya da Soyayya Kaunar Zuci, da Sai A Lahira, da Dan Adam Butulu, da sauran su, wadanda za a iya cewa sun fito daga gun kwararrun da muke da su ba sa wani tasiri a tsakanin sauran finafinai da 'yan koyo ko kuma marasa kwarewa suka yi.
d) Dattawa
A watannin baya da suka wuce, Alhaji M.D. Yusuf ya kira wani taro na 'yan fim inda yake nuna cewa yana so su ilmantar da shi a kan wannan harka saboda ya jahilce ta. A nawa ganin, da wani ne daban da ba shi ba ya yi wannan yunkurin, to da sai a yaba masa. Amma duk wanda ya duba matsayinsa a Arewa, zai fahimci cewa abin takaici ne a ce bai san inda harkar finafinan Hausa ta dosa ba, bayan kusan shekaru 13 da fara su. To ba shi kadai ba, akwai sauran dattawa irinsa daga cikin sarakuna da manyan ma'aikatan gwamnati, da 'yan siyasa, da kuma manyan 'yan kasuwa wadanda ba su taba tsayawa daidai da rana daya sun kalli fim din Hausa ba, duk kuwa da yake suna Hausawa. Sai dai kuma duk irin wainar da ake toyawa a Hollywood, da Bollywood da kuma Hong Kong suna sane da ita. Kodayake akwai wasu daga cikinsu da suke cewa a da, sukan kalli wasannin kwaikwayo da akan yi a gidajen talabijin, musamman da yake sun fi tsari, sannan kuma 'yan wasan sun kware. Bayan nan kuma ana iyakar kokari a nuna yadda al'adun Bahaushe suke na gaskiya. Su kuwa finafinan da ake yi na yanzu sam ba abin da suke sai dauka bakin al'adu na wasu kasashen.
Sai dai kuma kash! Su kansu na da din da ake yabon su, me aka taba tsinana masu? Wa ya taba tunanin a ware wata rana guda, don a tuna da mashahuran 'yan wasan kwaikwayon da suka shude kamar su Shariff Lawal (Karo-Da-Goma), da Mansur Kwalli (Gaso Rogo), da Hajiya Kulu (Kandala), da Dala Bakori (Bariki) da sauran su wadanda suka shude? Su kansu kwararrun da Arewa take ji da su kamar Adamu Halilu (Kanta of Kebbi), da USA Galadima (Soyayya kunar Zuci), da Tijjini Ibrahim (Mukaddari) da sauransu, wa ya damu ya tuna da su? Idan har ba a tunawa da wadannan yaushe za a tuna da Aminu Hasan (Ajizi), da Balaraba Mohammed (So)? Yanzu wa ya damu ya san halin da suke ciki? Malam Muhammad Mustafa (Malam Mamman yana nan a raye, sai dai ba ya ji kuma ganin nasa kadan ne). Alhaji Daudu Suleiman (Kuliya Manta Sabo) shi ma yana nan. Ga su Usman Baba Pategi (Samanja), da Kasimu Yero, da Umar Danjuma Katsina (Kasagi), wadanda duk suna nan da ransu amma Bahaushe ya manta da su. Shi ya sa ma wadanda suke cikin harkar a yanzu suke yin harkokinsu gabansu gadi, saboda suna ganin ba wanda ya damu da su, don haka su ma ba su damu da kowa ba.
Shi kansa wannan taro da aka shirya, akwai irin fassarar da kowane dan fim yake yi masa. Wasu na ganin cewa an shirya shi ne don a kwace musu hanyar neman abincinsu. Wasu kuma gani suke an shirya shi ne don a kawo gyara yadda kowa zai amfana. Ni kuma gani nake yi cewa cikin biyun nan akwai daya. Ko dai riga-Malam masallaci ake kokarin a yi, ko kuma fargar Jaji. Abin da ya sa na ce riga-Malam masallaci shi ne, don an fara ganin Turawa suna rige-rigen zuwa kasar nan domin nazarin finafinan Hausa, alhalin ga wadanda alhakin abin ya rataya a wuyansu sun yi biris da shi. Idan ba a manta ba Brian Larkin ya zo ya yi bincike a kan finafinai, haka ma Fredrick Noy. Yanzu kuma ga Mathias Kirgs shi ma ya taho. Ban da kuma saura da suke tafe nan gaba.
Wani abin mamaki game da Dokta Mathias shi ne a lokacin da na yi hira da shi na tambaye shi cewa kamar yanzu finafinai nawa ya kalla da zuwansa kasar nan? Sai ya ce min kamar guda 40! Lokacin da muka yi wannan hira bai wuce kwana 20 ba da zuwa kasar nan. A nan zan iya bugar kirji na ce a yanzu haka akwai wani daga cikin manyanmu da bai taba kallon fim din Hausa ba. Wato dai za a koma 'yar gidan jiya, kamar yadda ta faru da harshen Hausa, inda aka shafe wani tsawon lokaci ana tafiya Ingila da Amurka don a yi nazarinsa.
e) Jami'o'i
A nan ina nufin gungun masu iliminmu da ke dankare a Jami'o'in kasar nan, wadanda kuma suna da nasaba da harkar finafinai ko ta ko'ina. Babban laifinsu a wajena shi ne, har yau har gobe ba su ma san halin da ake ciki ba game da finafinan Hausa. Idan ka je sashin koyar da harshen Hausa, da kuma na ayyukan sadarwa na Jami'o'in Arewa za ka tarar ba a nazarin wadannan finafinan, balle har a yi wasu rubuce-rubuce a kan su. Kuma a iya sanina, babu wani cikakken littafin da wani masanin Hausa ya rubuta (wanda ba kundin bincike ba) da yake nazarin finafinan Hausa, ko da kuwa kushe da hassada ne. Su kansu daliban da ake koyarwa ana nuna musu cewa wadannan finafinai da ake yi, shirme ne kawai. Don haka kada su kula da su. Kuma babu su a cikin tsarin koyarwa na yawancin jami'o'inmu. A yau babu Furodusa ko Darakta guda daya rak, daga Jami'ar Bayero ta Kano da ya taba shirya wani fim din Hausa. Haka kuma babu wani Darakta ko dan wasa da za a ce an yaye shi ya shiga wannan sana'a daga nan.
Akwai wani lokaci a 1993-94, an bullo da wani kwas a cikin sashen harsunan Nijeriya da Afirka na Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, da ake kira 'Simple Dramatic Performance' da kuma 'Complex Dramatic Performance', inda ake son a koya wa dalibai yadda za su dinga yin wasannin kwaikwayo a dandali, ba wai kawai a zauna a aji ana karantawa ba. A lokacin an dauko Umaru Danjuma Katsina don ya dinga koyar da wannan kwas. Amma abin mamaki, sam abin bai yi tasiri ba, domin yawancin dalibai suna ganin wannan harkar kabilu ce don haka ba ta shafi Bahaushe ba. Ko ma da wane hali ake ciki, na tabbata wata rana za a ji kunya idan har aka bari wadanda ake masu kallon ba su san komai ba suka ci gaba da jan ragamar shirya finafinan Hausa. A yanzu haka idan ana maganar finafinai a Nijeriya, sai dai a yi zancen na 'yan kudu, saboda ba wani abu da masu iliminmu suke rubutawa game da su.
Abin da ya sa na ce kuma fargar jaji shi ne don sakacin da muka yi tun lokacin da guguwar wadannan finafinai ta taso ba mu yi wani abu a kai ba, sai yanzu da muka ga sun fara yin wani tasiri (mai kyau ko mara kyau) a rayuwarmu da ta iyalanmu. Sannan kuma sai da muka ga wasu sun fara tunanin watakila al'adar Bahaushen da ake nunawa a cikin wadannan finafinai, ita ce ainihin al'adar Bahaushe na zahiri. Yanzu ne da aka riga aka fille mana kawuna, sannan muka farga.
Menene abin yi?
Idan ana biye da ni za a fahimci cewa ina kokari ne na bayyana dalilan da suka sa finafinan Hausa suka samu kansu a halin da suke ciki da kuma wadanda suka jefa su a cikin wannan hali. Fatarmu ita ce a samu sauyi ko yaya yake a kan yadda ake ma wadannan finafinai mummanar fahimta. Ga kuma yadda nake ganin ya kamata a yi:
1) Gwamnati ta kawo dauki:
Gyara tsarin tace finafinai yadda duk fim din da bai dace ba, kar ya shigo kasuwa.
Karfafa wa masu harkar gwiwa ta hanyar shigo da wata gasa ko hanyar yabo, ta yadda duk wanda ya yi fim din da ya dace, zai samu wata kyauta ko yabo na musamman.
2. Taimakon Malamai:
Su fara nazarin finafinai da idon basira don su gano ainihin abubuwan da ba su dace ba ta yadda za a gyara. Su dinga gayyatar masu shirya finanfinai don su jawo hankulansu a kan abin da suka gani a cikin wani fim wanda kuma bai dace da Musulunci ba. Haka kuma su dinga taimaka wa masu yin fim da shawarwari a kan duk wani labari da aka rubuta kafin a mayar da shi fim.
3. Kwararru sai sun sa hannu:
Dole ne su fito su karbi ragamar al'amura a hannunsu, su daina shayin fitowa a yi gogayya da su. Watakila ma ta haka za su nuna bambancin da ke tsakanin kwarewa da rashinta.
Su shigo da wasu hanyoyi na taimaka wa wadanda ba su nakalci harkar ba, ta shigo da wasu kwasas-kwasai ko bitoci na sanin makamar aiki, kamar dai yadda marigayi Tijjani Ibrahim ya dinga taimaka wa wasu daga cikinsu yi kafin ya rasu. Ba da shawarwari a kan irin kayan aikin da suka kamata a yi amfani da su wajen shirya finafinai don a fara samun inganci.
5. Kirkiro sashen koyar da finafinan Hausa a Jami'o'in arewa.
Don a fara nazarinsu. Don a fara samun kwararrun 'Yan wasa, da Furodusoshi, da kuma Daraktoci. Don sana'ar ta samu alkibla kamar sauran sana'o'i.
6. Kafofin watsa labarai za su iya taimakawa
Ya kamata a ware wani lokaci ko da sau daya na nuna finafinan Hausa a gidajen talabijin na kasar nan. Musamman ma dai wadanda suka dace da al'adunmu da addininmu.
Ko kuma a bullo da wani shiri na sharhin finafinan Hausa ko da ba za a nuna su ba. Wato dai kamar shirin da a kan yi a gidajen talabijin na kudancin kasar nan (I'Agbo Video and Bayowa Films Half hour NTA 7, Tiwa N'Tiwa LTV 8: movie Half Hour NTA 2 dss).
7. 'Yan kasuwa su shigo su zuba jari
Don su bunkasa sana'ar. Idan har sana'ar ta bunkasa, kwararru za su shiga ciki su bunkasa hanyoyin kasuwancin finafinai domin hanyoyin da ake bi yanzu ba su da inganci.
8. Masu shirin fim na yanzu su gane kurensu, da kuma irin kalubalen da ke gabansu, sannan kuma su rage girman kai. Su sani cewa duniya ta zuba musu ido, duk abin da suka fito da shi a matsayin al'adar Bahaushe a cikin finafinansu, to fa da shi za a yi aiki.
Su dinga sanin yadda za su girmama addini ta yadda ba za su dinga cutar da shari'ar Musulunci ba. Ya kamata su san irin shigar da za su dinga yi da kuma ire-iren kalmomin da za su dinga fada. Su riki sana'ar su da muhimmanci. Su dukufa neman ilimi musamman a fagen sana'ar da suka sa a gaba. Su dinga hada kai da junansu, domin rarrabar kawunansu na daga cikin abubuwan da suka jawo ake kushe su. Ya kamata su dinga saurarar shawarwarin magabatansu.
A karshe zan iya cewa ba nufina bane a wannan taro na kushe kokarin da aka fara yi don ciyar da finafinan Hausa gaba, sai dai ina so ne na nuna mana yadda mummunan zato da sakaci suke da illa a duk harkokin da muka sa a gaba. Haka kuma kushe abu ba tare da kawo mafi kyawunsa ba, shi ma wata illa ce mai zaman kanta, wadda takan hana mu ci gaba. Domin idan har za a kushe abu, kuma ba a kawo wani a madadinsa ba, to an haddasa illoli biyu - an dakushe zuciyar wannan da yake yi, sannan kuma an kasa yi. An yi biyu babu kenan!
Komawa babban shafinmu Komawa saman wannan shafin
|
|