Jaridar Bunkasa Kasuwanci da Siyasa
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Labarun Gida

An yi bikin yaye dalibai a UNDP Samaru

Daga Shu'aibu Samaru

A kwankin baya ne makarantar koyon sana'a da ke garin Samaru Zariya a Karamar Hukumar Sabon gari ta Jihar Kaduna, ta yi bikin yaye dalibanta da suka kammala karatunsu, su kimanin 480, cikin fannoni daban-daban, kamar abin da ya shafi dinki, saka, walda, kafinta, gyaran famfo da kuma na'ura mai kwakwalwa da dai sauransu.

Taron ya sami halartar manyan baki da dama, duk da cewa da yawa daga cikinsu ba su sami halarta ba wasu kuma daga cikinsu sun turo wakilansu, wasu kuwa sun sami amsa wannan gayyata. Cikin wadanda suka sami halarta sun hada da Ambasada Sule Buba da Kwamishinan gona, Alhaji Lawal Sama'ila Yakawada da Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari Alhaji Bashir SakadadiI da Hon. Aliyu Manchester da dai sauransu.

Shi kuwa Gwamnan jihar Kaduna bai sami halarta ba turowa ya yi. Wanda ya turo shi ne Kwamishinan ciniki da masana'antu, Alhaji Muhammad Baba Zariya. Sai kuma uwargidan Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asma'u Makarfi da ba ta sami zuwa ba ta turo Hajiya Binta Ayuba wadda ta wakilce ta, da dai sauran manyan baki.

Da farko dai bayan an bude taro da addu'a an dai sha wakoki daga mawaka daban-daban, sai Ambasada Sule Buba ya tashi domin yin jawabin maraba. A cikin jawabinsa ya nuna irin kokarin da gwamnati take yi don ganin ta yi maganin zaman banza. Domin ya ce babu wata Karamar Hukuma ko jiha ko gwamnatin Tarayya da za ta ba kowa aikin yi, amma kafa wadannan makarantu don matasa su taimaki kawunansu zai taimaka. Ya kara da cewa daliban wannan makaranta da aka yaye za su ba da matukar gudummawa. Ya kuma ja kunnen 'yan siyasa don su tallafa wa irin wadannan makarantu da kayan aiki.

Shi kuwa Shugaban wannan makaranta ya nuna farin cikinsa da godiyarsa ga Allah ganin yadda ba a sami rikici ko wani tashin hankali ba a wannan lokaci da yake kan wannan kujera. Ya kuma mika kokensa ga gwamnatin jihar Kaduna domin ta taimaka wa wadanda aka yaye a wannan makaranta.

Shi kuma Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari, Alhaji Bashir Sakadadi ya mika godiya ne ga uwargidan Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asama'u Makarfi ganin yadda take taimaka wa marasa galihu, musamman ganin yadda a kwanakin baya ta ba da makudan kudade ga jama'a.

Shi kuwa Kwamishinan ciniki da masana'antu ya mika sakon gwamnatin jihar Kaduna ne, a inda yake cewa gwamnatin jihar Kaduna tana mika godiyarta ga Majalisar Dinkin duniya da ke taimakawa ga irin wannan makarantu. Alhaji Muhammad Baba Zariya ya yi wa jama'a albishir cewa daga cikin irin aikace-aikacen da gwamnatin jihar Kaduna take da shi akwai shirin da za a yi don a taimaka wa masu sana'a'o'in hannu don su kafa masana'antu. Akwai kuma wani shiri da za a yi wanda zai taimaka wa kananan 'yan kasuwa don su dogara da kansu.

Ya kara da cewa akwai kuma wani shiri da aka fito da shi domin mata kawai a kowace Karamar Hukuma. Don haka ya ja hankalin matan wannan Karamar Hukuma da su je su bincika domin su ci gajiyar wannan shiri.

Daga karshe ita hukumar wannan makaranta ta karrama wadansu mutane da dama, musamman wadanda suka taka rawar gani domin wannan makaranta ta ci gaba. Cikin wadanda aka karrama akwai Gwamnan Kaduna, Ahmad Makarfi da uwargidansa Hajiya Asma'u Makarfi da Ambasada Sule Buba da Kwamishinan ciniki da masana'antu Alhaji Baba Zariya da Kwamishinan ayyukan gona, Alhaji Lawal Sama'ila Yakawada da Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari, Alhaji Bashir Sakadadi da Alhaji Aliyu Ahmad Manchester da dai sauran su.

Masu ci rani su sanya 'ya'yansu a makaranta

- Sarkin Hausawan Gwagwalada

Daga Bello Hamza

Sanin kowa ne a kowane gari ko birni, musamman ma garuruwan kabilu na wannan kasa, akan sami baki wadanda suka je suka zauna domin ci rani ko kuma zama dindindin da iyalinsu. Idan zama ya yi dadi har sarauta ake makala masu, daga karshe dai sai ka ji sun zama 'yan gari, sai ya zama gidajensu ya koma masaukin baki wadanda ba su san kowa ba. Don irin wadannan dalilan ya sa Dillaliya ta ziyarci Sarkin Hausawan Gwagwalada Alhaji Sani Daika.

Wakilinmu ya tambaye shi ko shi mutumin ina ne? Sai ya ce, "ni asalina Basakkwace ne a Kkaramar Hukumar Gwaranyo."

Wakilinmu ya tambaye shi ko ya gaji sarautar ne? Sai ya ce shi bai gaji sarauta ba, amma dai tun yana karami yakan tausaya wa jama'a, yana kuma taimakon su. Saboda irin dabi'unsa da kuma ganin yadda yake yi da jama'a, sai wani kakansa ya ce a sanya ido a kan wannan yaro a nan gaba zai zama wani abu.

To Allah cikin ikonSa, da Sarki ya shigo bariki, sai ya ci gaba da dabi'unsa na taimakon jama'a kamar yadda ya saba. Ana cikin haka. sai Allah ya ba shi sarautar wannan gari na Gwagwalada.

Kan dangantakar Hausawa da sauran kabilu, Sarkin ya ce lallai suna da kyakkyawar dangantaka da fahimtar juna, kuma dukkansu sukan girmama junansu, duk da cewa Hausawa sune mafiya rinjaye a wannan gari. Kuma a sarauce sakamakon sarautar Sarkin Hausawa ne, to wannan ya sanya suna yi wa sarautar Gwagwalada biyayya, domin duk abin da Sarki ya ce su yi suna yi, idan ya ce su bari suna bari. Kuma ba a taba samun wani rashin fahimta a tsakaninsu ba. Haka kuma sauran kabilu wadanda ba Hausawa ba, ba sa nuna masu wani bambanci.

Alhaji Sani ya kara da cewa yana so ya ja kunnen masu zuwa ci rani cewa duk wanda zai baro gidansu ya zo bariki, to ya san sana'ar da zai yi. Kada ya zo ya zauna ba shi da aikin yi domin zaman banza ba abin yi bane. Kuma su wadanda suka zo har Allah Ya ba su iyali ko suka zo da su har kuma suka sami yara, to a yi kokari a sanya yaran a makaranta, domin yin haka shi ne taimakon yara, ba a bar su kara zube ba, su lalace, su rika bin yara suna shaye-shaye.

Daga karshe Alhaji Sani Daika ya ja kunnen Hausawa mazauna Gwagwalada cewa su zauna lafiya da abokan zamansu. Kuma ya ce shi zaman lafiya shi ne rayuwa, kuma duk wanda jama'a suka ga ba su gane masa ba, to su kai karar sa. Kuma ya ja kunnen jama'ar kasar nan da su zauna lafiya.

Shekara daya na Gwamna Ibrahim Shekarau abin yabawa ne

Shekara daya da Gwamna Ibrahim Shekarau na jihar Kano ya yi abin yabawa ne matuka, idan aka yi la'akari da irin gina hanyoyi da yake yi a birnin Kano da kuma karkara, ga kuma kula da yake yi wajen samar da ruwan sha, ba da wutar lantarki da kuma inganta kiwon lafiya.

Wannan jawabi ya fito ne daga bakin Shugaban Karamar Hukumar Bichi a jihar Kano, Alhaji Lawan Shehu a lokacin da yake zantawa da 'yan jarida a ofishinsa da ke Bichi, inda ya ci gaba da cewa, "duk maganganun da 'yan hamayya ke yi a kan rashin tabuka komai tun hawa kan karagar jihar Kano na Malam Ibrahim Shekarau, rashin adalci ne ta bangaren 'yan hamayya."

Da ya juya ta bangaren gwamnatin tarayya kuwa, Alhaji Lawan Shehu ya yi kira ga gwamnati da ta rika bai wa Kananan Hukumomi kason kudadenta kai tsaye ba tare da ta biyo ta hannun gwamnatocin jihohi ba, domin bai wa Kananan Hukumomi kasonsu kai tsaye zai kawo ci gaba sosai ta fannoni da dama.

Ya kara da cewa, Karamar Hukumarsa ta Bichi ta himmatu sosai wajen samar da ruwan sha, kiwon lafiya da kuma kula da tsaro a dukkan fadin Karamar Hukumar, wanda a yanzu haka har an fara kakkafa rijiyoyin burtsatse guda uku.

Sa'annan ta fannin kiwon lafiya ana wadata dukkan dakunan shan magani da magunguna, haka kuma yana samun cikakken hadin kai ta fannin tsaro wajen 'yan sanda da kuma DPO na Karamar Hukumar.

A karshe, Alhaji Lawan Shehu, ya yi kira ga al'ummar Karamar Hukumar, da su ba shi hadin kai ta yadda zai ji dadin gudanar da ayyukan Karamar Hukumar, domin ta haka ne Karamar Hukumar za ta sami ci gaba.

Komawa babban shafinmu                                   Komawa saman wannan shafin