Talaka babban mutum
A rubutun da na yi na baya-bayan nan, a wannan fili mai kanu SIN DA SINAWA, na nuna irin bakar wuyar da aka tilasta talakawa sha, lokacin da wani Sarkinsu ya sa suka gina katangar Sin, wadda aka ce tsawonta kamar misalin daga Katsina zuwa Legas ce, sannan bisanta sai ka cire hula ka dafe keya kafin ka iya hango karshenta. Abin da ban fada ba ma, wanda daga baya na gano shi ne kaurinta a can sama, wanda aka ce dawaki ingarmu goma sha biyu na iya sukuwa a kanta ba tare da wani ya kuntatawa wani ba, balle ma har ya turo shi kasa.
Duk dai a cikin wancan rubutun, na ce irin wannan bakar wuya ce talakawa suka sha, ko kuma in ce aka tilasta musu sha a wajen gina kabarin tsinanne la'anannen Allah, Fir'auna, wanda saboda tsabar mike kafa a kan talakawansa da shakar iskar mulki ya yi da'awar shi Ubangiji ne, ya kuma yi iyakar kokarinsa wajen shiga tsakanin mutane da Annabi Musa (A). Har ma da kokarin halaka shi baki daya. Amma bayan halakar da Fir'auna, sai mahukuntan Misira suka yi amfani da talakawa wajen gina masa da sauran Fir'aunonin Misira kabari. Saboda tsabar yadda aka bautar da talakawa a wajen samar da shi, a yau yana daya daga cikin abubuwan da mutane daga ko'ina a duniya ke tururuwar zuwa kallo. Kuma yana daya daga abubuwan ban mamaki da duniyar yau ke tallatawa.
A wancan lokacin har ma na yi wa makaranta wannan filin tambayar cewa shin ko wannan yanayi na bautar da talakawa domin sama wa duniya abin mamaki ya tsaya ne daga wadancan mutane da lokutansu ya shude? Ko kuwa da kidan duniyar ta sauya, sai su ma rawar mahukuntanta ta canza? Har na ce ina ganin da kidan duniyar ta canza sai su ma rawarsu ta canza. Har kuma na ce a rubutu na gaba zan kara bayani bakin iyawata.
Sai dai ba zan ce na sauke wancan nauyi da na dora wa kaina ba ta hanyar wannan rubutun mai kanu; TALAKA BABBAN MUTUM. Sai dai zai taimaka wajen wayar da kan 'yan uwana talakawa su san kansu, ta yadda za su iya zama masu amfani ga Mahaliccinsu, kasarsu da al'ummar da suke rayuwa a cikinta. Ba kuma tare da an rataya musu sarkar bauta ba.
Ina ganin zan sauke wancan nauyi ne a rubutu na gaba wanda zan yi hususan a kan irin wahalar da talakawa suka sha wajen samar da kabarin Fir'aunonin Misira da ire-irensa wadanda a yanzu ake kira abubuwan ban mamaki a duniya.Yanzu sai mu dawo kan maudu'inmu, TALAKA BABBAN MUTUM.
"Talaka babban mutum?", tambayar da na san wani zai yi kenan, kafin ya fara karanta wannan mukalar. Wani kuma cikin tuhumar yadda za a ce wa talaka babban mutum, zai karanta ta. Hatta talakan da bai san ko shi wanene ba a tsarin al'ummar da yake cikinta ba zai yarda a kira shi babban mutum ba.
Da farko kafin mu yi nisa ya kamata mu san wanene talaka? Talakawa sune sauran jama'a wadanda babu mulki a hannunsu, imma na gargajiya ko na zamani, kamar masu rike da mukamai na siyasa ko kuma babban mukami a gwamnati. Sai dai a wasu lokutan, mai kudi ma yakan fita daga ajin talakawa, saboda alfarmar kudinsa. Wannan a bayyane yake ga Hausawa, domin har karin magana suke da ita mai cewa "Mai kudi aminin Sarki" ko "Mai kudi kamar wani Sarki." Idan mun yarda da wannan fassarar, kenan za mu iya cewa talakawa su ke da zunzurutun yawa a cikin kowace al'umma. Domin kuwa su yallabai za ka iya kirge na garinku. Kai har ma alkaryarku, amma ka yi kadan ka kirga talakawan garinku, in dai garin na da girma balle kuma na alkaryarku.
Saboda haka, ni a fahimtata, talaka shi ne babban mutum domin kuwa duk wani nau'in abin kaiwa bakin salati da ka gani a karkara, ko cikin birni, shi ne ya samar da shi. Ka ga a nan yana da lada ninki biyu, ga shi dai ya kulle 'yan kwabbansa, ga kuma ladan ciyar da al'umma. Abin da Hausawa ke cewa "Nagge dadi goma."
Idan ka shiga cikin birane, duk wani gini da ka kalla, ka kara kallon sa, saboda kyawunsa ko tsawonsa sai da talaka ya sa hannu sannan aka samar da shi. Ko za ka gaya min wani gida wanda aka gina shi ba da Leburori ba? Duk hanyoyin da Julius Berger ke shimfidawa a cikin duwatsu da ruwa, da gine-ginen ban mamaki a cikin birane, sai da talaka ya shigo ciki ya taimaka sannan hakan ta yiwu. Duk kwazon Injiniyoyi da dimbin na'urorinsu idan babu Lebura aiki ba ya zuwa ko'ina. Ina ganin ma duk wata harka ta kasuwanci ko zamantakewa, dole ne a samu talaka a cikinta. Kila ka ce min ai duk wadannan ayyukan wahala ne. Saboda haka ba su isa mai da talaka babban mutum ba, tun da za a ce garin neman na kaiwa bakin salati ne ya yi su. Kuma ma ai bukatarsa ta biya tun da an ba shi ladan aikinsa. To na ji, mu koma batun aikin hutu da kuma mike kafa, a tsari irin na damukukkurda, wai Dimokradiyya. Masu dogon hanci da tsawon gashi, wadanda sune suka samar da abin, sun ce; "A voter is a king maker," wato mai zabe shi ne mai nadin Sarauta.
Kuma idan ka yi la'akari da fassarar da muka ba talakawa za ka iya yarda da cewar sama da kashi casa'in cikin dari na masu kada kuri'a talakawa ne. Ka ga kenan talakawa ne ke da wuka da nama a wajen zaben shugabanninsu tun daga kan Kansila har zuwa kan Shugaban kasa. Kuma sune ake wakilta, sannan da yawunsu ne ake yin mulki.
Kuma lura da wani abu guda, idan zabe ya matso duk masu neman wadancan mukamai da na fada, wato daga Kansila zuwa kan Shugaban kasa, za ka ga sun rude sun kidime sun bazama a mazabunsu lungu-lungu da sako-sako, suna lallashin manyan mutane talakawa. Har sai sun hada da ba su na goro da yi masu alkawura daban-daban, domin dai kawai su daure su dubi dawainiyarsu su nada masu rawanin shugabanci.
Na shiga tawagar kamfen din wani dan siyasa, amma a matsayina na dan jarida, domin in ga wainar da ake toyawa. Mun shiga lunguna da dama, wasunsu ma babu ko hanyar mota sai dai mu banki geza da sabara mu wuce. Irin wahalar da na ga ana sha tana da yawa. Ga dai na kudin abinci, sayen man motoci da ba duk mutanen da aka iske a garinsu kudin sayen goro, tare da ba su hakurin cewa kudin ba yawa, ga dimbin lokacin da ake batawa. A wannan fita da aka yi da ni, da muka fita tun da safe sai da muka kai karfe biyu na dare, sannan muka dawo gida. Ni kam daga ran nan na sare. Su kuwa suka ci gaba kuma dama kafin a fita da ni sun yi wasu kwanakin suna fita. Duk fadi da tsawon mazabar dan takara, sai ya san ta kamar tafin hannunsa saboda gewaya ta ninkin-ba-ninkin da zai rika yi, idan har yana son ya ci zabe. Da na tsaya na yi wani dan guntun lissafi a kan abin da ake kashewa kafin a ci zabe, sai na fahimci cewa abin ba na wasa bane. Domin kuwa kudin ba 'yan kadan bane, kuma na san duk wadannan kudaden ba su cikin abin da 'yan siyasa ke cewa; "kayan aiki." Su kayan aiki sai kusa da zabe ake fiddo su, kuma su ma makudan kudi ne. Yawansu ya danganta da yawan mazabar dan siyasa.
Kwanan nan na je wata tsangayar 'yan siyasa na ji suna cewa; "saboda irin yadda aka bata talakawa da siyasar kudi, a yanzu duk wanda ke son zama Shugaban Karamar Hukuma, kuma ya yi sa'a mutane shi suke so, to ya tanadi Naira miliyan biyar, "kayan aiki gab da zabe."A ra'ayinsu sai ma idan shi talakawa ke so, idan kuwa ba shi ake so ba, yana so ne ya rinjayi mutane da kudi, to sai dai ya tanadi ninkin-ba-ninkin na wadannan kudin.
Na ji takaicin jin haka, na kuma tausaya wa 'yan uwana talakawa a kan abin da zai same mu idan aka gama cinikin 'yancinsu, aka kuma saye kudi hannu, Allah wadan naka ya lalace! Mu sani fa mutanen nan ('yan siyasa), kamar bebin roba ne a hannunmu talakawa idan wa'adin mulkinsu ya kare suna son kuma su yi "TAZARCE," ko kuma idan suna son a goya masu baya "TA-LANKWASHE."
A Bauchi na san Kansilan da aka ce ya fashe da kuka da aka rika shakkar fitar da shi ya yi takara a zaben Kananan Hukumomin da ya gabata. Amma daga bisani an amince masa ya yi takarar kuma ya ci. Sai dai ka san abin da ya faru bayan sun zabe shi, mutanen mazabarsa sun tabbatar wa MAZARI cewar bai yi wa mazabarsa wani abin a zo a gani ba, amma fa ya samu nasarar arzurta kansa, inda ya yi wurgi da dan keken da ya mallaka, ya sawo dankara-dankaran motocin hawa har guda biyu, ya gina gidaje, ya kara mata, ya kece raini iya son ransa. Don haka, ya kamata mu san abin da za mu yi da kuri'unmu a daidai lokacin da ake neman su. Shin za mu ba da su ne domin dorewar mulkin wanda bai kula da jin dadi da walwalarmu ba, ko kuwa za mu sauya shi da wani mai hali irin nasa? Ko ko yaya ya kamata mu yi? Muna da wani zabi na gari ko ko ba mu da shi?
Na ga motar sama da Naira milyan biyar jif, dankareriya ana ta ratsa kalgo da sabara da ita, ana lallashin talakawa da su yarda su amince wa mai ita su tura shi Abuja domin ya wakilce su a majalisar kasa. Wannan na nuna tasirin talakawa a wajen lamurran tafiyar da kasa. Eh, na yarda ana yin murdiyya a wajen zabe, talakawa su zabi wani amma a musanya musu shi da wani ta hanyar magudi. Amma ai an yi kadan a fito fili a ce; "ya ku talakawa ga wanda kuka zaba, amma mu mun ga ba shi ne ya cancanta ba, saboda haka mun musanya maku shi da wane." Haba! Wa ma ya isa ya yi wa babban mutum talaka irin wannan maganar?
Kuma ko magudi da "cushe" da ake yi, ai yana yiwuwa ne kawai a inda ra'ayin talakawan ya rabu. Amma idan da za su dunkule su zama tsintsiya madaurinki daya a kan wani ra'ayi, to ai babu ja, wannan ra'ayin shi ne za ya tafiyar da al'ummar dukkanta.
A nan zan ba ku wani dan labari da ke nuna karfin ikon talakawa wanda na ji a bakin manya.
Wani lokaci an yi wani gawurtaccen zakara wanda tozonsa ya gawurta sosai, jansa ya yi ja kamar garwashin wuta. Sai ya taka takanas ta Kano ya je garin muzurai ya ce masu ya zo ne domin ya mulke su, ko su yarda ko kuma ya sa wutar da ke kansa ya kone su duk! Da jin haka, sai duk suka mika wa zakara wuya cikin rashin sanin cewa tozonsa nama ne ma kawai ba wuta ba. Da haka ya yi ta jan su kuma suna bin sa kamar rakumi da akala. Wannan gawurtaccen zakara ya ji dadin wannan mulki, domin kuwa muzuran da magunansu na matukar tsoron sa. A kan haka ne kuma suke yi masa biyayya, ko kara ya gitta ba sa tsallakawa. Ga shi kuma suna yi masa dukkan abin da yake bukata na jin dadinsa da walwalarsa.
Ran nan zakara na barci a kan benen da suka gina masa, su kuwa talakawansa muzurai na ta kaiwa da komowa a kasa. Can sai wani muzuru ya tono wani abu da yake son ya gasa domin ya ji dadin cin sa, ya nemi wuta ya rasa. Can sai wani muzuru mai dabara ya ce ai ga wuta can a kan Sarki me zai hana ka lalaba yana barci ka dan dosano ka zo ka kunna wutar ka gasa? A nan wannan labari ya so karewa, domin kuwa shi wannan muzuru mai abin gasawa ya kasa tarbar aradu da tsinin ka. Can sai wani matashin muzuru daga cikinsu ya ce shi zai je ya dosano ta yadda kuma ba zai ta da Sarki ba.
Kafin ya tafi sai da suka gargade shi da cewar ya yi hattara, kada ya ta da shi ya jawo masu fushin Sarkinsu.
A haka ya tafi, yana zuwa kuwa ya lakato, sai ya ji taushi, ya sake lakata ya ji ashe ma dai tsokar nama ne kawai kwance, su ba su sani ba. Sai nan da nan ya dawo ya shaida wa abokansa. Ai nan da nan maka-Malam sai Sarki ya bi ta taga ya cika wandonsa da iska. Mai karatu don Allah ka ba mutanen Alaban Rago, shahararriyar kasuwar dabbobin nan ta Legas wannan dan guntun labari. Kila idan ka yi sa'a da mai dogon baki irina zai ba ka wani labari makamancin wannan da ya taba faurwa a kasuwar. A siyasar ma talakawa sun sha hada wa masu mulki "jini da majina." A Kano ba ku ga yadda suka dakatar da Kwankwaso daga mulki ba? Sun yi irin haka ma a wasu jihohin, sun kuma sauke masu mukamai daban-daban. Shugaba na cikin mulkinsa yana jin dadinsa, su ce masa ba su gamsu da abin da yake yi ba, saboda haka ya dawo gida ya zauna, su tura wani, kuma shi ma su ga kamun ludayinsa.
Hatta mutanen da tarihi ke kallon su a mutunce da kuma girmamawa ba su samu wannan daukakar ba sai da suka daura auren zobe da talakawa. Misali, duk wani shaharrarren dan siyasa ba zai buda baki ya ce Malam Aminu Kano ba mutumin kirki bane, kowa na ta hankoron nuna shi ma fa wani dan karamin Aminu Kano ne, wai dai don talakawa su amince masa.
Har wayau, ba zan bar ka ba mai karatu, ba tare da na kawo ma karin hujjojin da za su nuna cewa talaka na da muhimmanci kuma babban mutum ne ba. Ka lura da gidajen masu mulki da wadanda dambunsu ya ji mai a wannan lokacin, sun yi kama da gidajen fursuna. Karafuna ne za ka gani garkama-garkama a kofofin karfe an killace su da shi. A waje ga masu gadi da kulakensu, wadanda su da ma barci a wajensu haramun ne. Can ciki kuwa "Oga"na kwance, mai yiwuwa ma har da karamar bindigarsa a karkashin filo. Duk da wannan tsananta tsaro, da wata jifa za ta fada kan kwanon gidan, sai kowa a gidan ka ga hankalinsa ya tashi.
Talaka kuwa wani ma a gidansa babu kyaure balle ma ya rufe. Idan kuwa lokacin zafi ya zo zai ma iya fitowa da tabarmarsa a tsakar gida, ko kofar gida ya kwanta ya sha iska daga Rabbil Izzati.
A mu'amala ma, mafi yawancin lokuta talaka ya fi iya mu'amala. Zai dai tsaya ku gaisa, cikakkiyar gaisuwa, irin gaisuwar nan ta Fulani wadda har kaji da sauran dabbobi sai an ji halin da suke ciki. Sannan zai sakar ma fuska, zai kuma halarci dukkan bukukuwanka na farin ciki, zai kuma zo ma jaje ko ta'aziyya. Ba kasafai wadanda dambunsu ya ji mai suke samun sukunin yin irin wadannan mu'amaloli da ke kara dankon zumunci ba da kuma samun lada mai tarin yawa.
Wasu rashin lokaci ne, wasu kuma kahon kasaita ne ke fito musu a sakamakon abin da suke da shi na dukiya, mukamai ko kuma baiwa. Irin wadannan ba su da dadin mu'amala sam, domin kuwa suna iya sanya kahon kasaita su tunkuyi talaka da shi a kowane lokaci ya rabe su. Idonsu yakan rufe su kasa bambance tsakanin wanda ya zo masu da budaddiyar zuciya da kuma 'yan maula ko neman alfarma. Su a wajensu mutumcin mutum shi ne ya kasance yana da kudi ko mukami ko kuma baiwa irin tasu. In ba haka ba, shi banza ne, kuma za su iya taka shi su murje, ko kuma su sa kahon kasaita su tunkuye shi. Allah (T) Ya kiyashe mu da kahon kasaita amin. Duk mai shi kuma Allah Ya karya shi! Masoya Annabi su ce amin.
A lura ba ina nufin wata illa ta same shi bane fa. Ina nufin Allah Ya karya kahon kasaitar. Ka ga ai dama ba a san mutum da kaho ba, idan kuwa har ka ga mutum da kaho, ai ka san ba lafiya. Domin kuwa hakan ya bambanta shi da kamanni na kamala ta mutane. Idan kuwa har wani mai yi masa fata ta alheri, mai alfahari da cikar kamalarsa ya yi masa addu'ar Allah Ya karya kahon da ke tare da shi, na kasaita, domin ya dawo a yanayinsa na mutane, ka san lallai masoyinsa ne, ko ba haka ba?
Wannan rubutu ba zai kammala ba, ba tare da kawo wani hadisi ba wanda ko da shi kadai ne na kawo tun da farko ban ce komai ba ya isa kwakwalwar kowa ta shiga cikinsa ta yi nazarinsa ta tsamo dimbin darussan da za su iya yi wa mutum jagora a mu'amalolinsa. Wata rana ne Manzon Allah (S) yana zaune tare da Sahabbansa sai wani Sahabi attajiri ya zo, daga bisani ya zauna kusa da Sahabi matalauci. Sai Manzon Allah (S) ya lura da wannan Sahabi da ya zo daga baya yana tattare suturarsa yana kuma matsawa kada ya rabi wancan Sahabi matalauci. Sai Manzon Allah (S) ya ce masa; "kana gudun kada ya sanya ma talauci ne, ko ko kana gudun kada ka shafa masa arziki ne?" Sai Sahabi attajiri ya ji kunya, ya kuma yi nadamar abin da ya aikata na rashin kyautata mu'amala ga Sahabi talaka, dan'uwansa a Musulunci. Sai ya ce; "Ya Manzon Allah gaya wa wannan Sahabi (matalaucin) na raba dukiyata kashi biyu na ba shi rabi domin ya zama fansa a kan abin da na yi masa." Sai Manzon Allah Ya gabatar da wannan tayi ga wannan Sahabi (matalauci). Sai ya ce; "Ya Manzon Allah sam ba zan karba ba, saboda kada ni ma dukiya ta sa ni in koyi irin halinsa (na kyamar mutane)." Saboda haka wannan fili na nasiha ga wadanda suka samu kansu a ajin wadanda ke mulki ko wadanda dambunsu ya ji mai, da su rika yin kyakkyawar mu'amala da sauran mutane talakawa, wadanda sune suka fi yawa a cikin al'umma.
Haka ga talakawa 'yan'uwana, mu mutunta 'yancinmu, mu sani sayar da shi ba riba ko kadan, sai ma faduwa a nan duniya da lahira. Kada mu kuskura talauci ya sa mu fita hayyacinmu, mu yi ta 'yan buge-bugen da za su sa mu bugar da aljannarmu tun a nan duniya. In ba mu sani ba mu sani, in mun sani mu kara sani cewar talauci ba nakasa bace, ba kuma aibi bane. Don haka kada ya sa mu zubar da 'yancinmu.
Komawa babban shafinmu Komawa saman wannan shafin
|
|