Jaridar bunkasa kasuwanci da siyasa

Dangane da jaridar dillaliya

Ka tuntubi jaridar Dillaliya

Karanta jaridar Dillaliya a taskarta

Ka sayi jaridar Dillaliya

Ka duba wasikunku

Za mu samar da burodi mai tsafta da dadi

In ji Alhaji Isiya Naniya

DILLALIYA:: Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu.

NANIYA: Sunana Alh. Isya Naniya. Ni haifaffen jihar Katsina ne, amma a Kaduna na girma. Yau sama da shekaru 20 kenan muke zaune a Rigasa. A nan na kammala karatuna. Daga nan na dan bude shagon sai da kayan 'provision', na kuma soma zuwa matatar mai (refinery) ina sai da kalanzir, har na samu babban mukami a kungiyar masu sai da kalanzir.

Daga nan kuma na yi tunanin me zan yi wa garina inda nake zaune, duk da dai dama mun ba su aikin kalanzir. Sai na yi tunanin bude wannan kamfani. Ba wai na kirkiro da wannan masana'antar don kashin kaina bane, sai don jama'an da nake tare da su da kannenmu da matasa marasa aikin yi. Shi ya sa muka bude wannan gidan burodi don mutane su amfana. In dai maganar burodi ne insha Allah an daina yi mana gori da ake cewa mu ba mu da komai, burodi ma sai mun je Jovad ko Abbey ko Nanet da sauransu. Insha Allah duk abin da ake samar da shi a gidan burodi za mu samar da shi. Kuma mun samu kwararrun ma'aikata da kuma wadanda suka yi aiki a wasu gidajen burodin.

DILLALIYA:: Ko ka taba sana'ar burodi ne?

NANIYA: A'a ban taba yi ba. Abin da ya sa na fara da kamfanin burodi na ga gorin da ake yi mana na cewa mu Rigasa ba mu da komai ya yi yawa. Sai na ga ai jama'a suna da sha'awar cin burodi mai kyau mai dadi da tsafta, sai na ga to bari mu fara da kamfanin burodi, kafin mu koma kan sauran kamfanoni.

DILLALIYA:: Kimanin ma'aikata nawa ka diba da za su fara wannan aiki?

NANIYA: Alhamdulillahi a halin yanzu dai ma'aikatan da suna nan sun kai mutum sama da 25. Kuma har yanzu muna ta sanar da matasa da su kawo sunansu. Kuma mun bude yanki-yanki muna neman karin wasu, ba ma 'yan Rigasa kadai ba.

DILLALIYA:: An yi wa kamfanin rijista?

NANIYA: Eh, hakika wannan kamfanin yana da rijista tun daga Federal har zuwa state da Local Government.

DILLALIYA:: Ko wane kira za ka yi wa 'yan uwanka masu kudi don su ma su rika taimaka wa matasa?

NANIYA: Lallai ina kira ga iyayena, yayyina, abokanaina da mu hada kai, mu zo mu yi kishin Rigasa ta hanyar da za mu gina ta. Ba ta wani wuri za ka gina garinka ba sai ta hanyar da matasa za su samu aikin yi. Kullum ana zargin matasa ana cewa ba su da aikin yi, ana cewa suna sace-sace, ba komai ya kawo wannan ba, sai don a yau idan mutum yana da aikin da zai yi, kuma yana yi, to ya fi gaban zagi. Don haka ina kira ga masu kudin Rigasa da su waiwaya su zo su gina garin nan. Ko da kasuwanci ne sai ka yi yadda wani matashi zai amfana.

DILLALIYA:: Ko akwai yiwuwar za ka sake bude wata masana'antar a nan gaba?

NANIYA: Eh, dama akwai wannan tunanin a tare da ni. Sai dai dama wannan na burodi shi ne na farko. In mun ga ya amsu sosai, to nan gaba za mu fara yunkurin bude wani kamfanin wanda ba jihar Kaduna ba, duk arewaci za su ci albarkacin wannan masana'antar in Allah ya yarda.

DILLALIYA:: Duk da dai ka fada cikin siyasa, ko me ya ba ka sha'awa?

NANIYA: A yanzu duk mutum mai son ci gaba sai ya bi ta fannin siyasa. Ni na shiga kogin siyasa ne don kishin Rigasa, saboda ana cewa mu 'yan Rigasa mun mai da Rigasa ta zama kamar 'lodging', mun mai da ita wurin kwana kawai. Sai dai mu kwanta kawai gari ya waye mu fita. Ba wata gudummawa da muke ba garinmu. Ba mu zabe, ba mu komai. Shi ya sa muke kokarin mu nuna wa jama'a muhimmancin siyasa da mu fito mu rinka yins a, kar a dinga barin mu a baya. Don mun ga kuskuren rashin fitowa zabe. Kuma shi siyasa in ka zabi mutum, to zai maka abin da kake so. Lallai mun gane kuskurenmu. Ina kira ga mutanen Rigasa da su sani fa ta hanyar yin siyasa ne za mu kwatar wa Rigasa 'yancinta, in dai muna son ci gaba.

DILLALIYA:: Jama'a na cewa kana da sha'awar tsayawa takara nan gaba, shin ko yaya gaskiyar lamarin?

NANIYA: Batun cewa ina da sha'awar tsayawa takara ba gaskiya bane. Ni dai babban bukatata, duk mutumin da zai kawo wa Rigasa ci gaba da zaman lafiya shirye nake da na mara masa baya. Ba wai muna yi bane don bukatun kanmu, a'a muna shirye da mu taimaka wa duk wani mai bukatar ci gaba a wannan jihar da kuma Rigasa baki daya.

DILLALIYA:: Yaya batun cewa gwamnati ba ta tsinana maku komai ba?

NANIYA: To a kullum in kana bukatar abu wurin gwamnati sai ka fito ka nuna mata kana bukata. Bai yiwuwa ka zauna kara zube ka ce gwamnati ta san ka. Kamar batun da ake cewa gwamnati ba ta yi mana komai ba, lallai mu ma kanmu ba mu yi wa kanmu komai ba. Daga wannan kowa ya san ba mu tsinana wa Rigasa komai. Ba ma mata komai. Ga kasuwa nan an gina ta ta rushe. Ba mu da asibiti inda marasa lafiya za su yi jinya, sai dai mu kai shi wajen garin rigasa. Karatun yaranmu sai dai wajen garin Rigasa. Da wannan dalili na cewa ba mu tsaya mun nuna kishin garin ba. Yaushe gwamnati za ta kula da mu ta san da damuwarmu? In mun tsaya tsayin daka, gwamnati za ta mara mana baya dari bisa dari. Mun gane kure, amma a yanzu za mu gyara, in Allah ya yarda gwamnati za ta san da mu.

DILLALIYA:: Wane kira za ka yi wa jama'a dangane da katin rijista da na zama dan kasa?

NANIYA: Lallai mu nan babban abin da muke ba da karfi a kai kenan. Muna kuma kira ga jama'a da su dage su ba da goyon bayansu. Kuma da zaran an fara wannan abin za mu dakatar da ayyukanmu don ganin cewa jama'a sun fito sun yi rijista. Mun shirya kwamiti na matasa don ba da karfi ga yin rijista. Za mu sanar a masallatai, makarantu da kasuwa da zaran an fara.

DILALIYA: Mun gode.

NANIYA: Ni ma na gode.


Komawa shafin farko