Jaridar Bunkasa Kasuwanci da Siyasa
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
RA'AYOYI

Obasanjo: Na yi da na sanin zaben ka

Daga Bello H. Abuja

Bayan mutuwar Janar Sani Abacha, Janar Abdussalami bai yi wata-wata ba, ya shiga shirye-shiryen mika mulki ga farar hula. Cikin watanni tara aka kafa da kuma yi ma jam'iyyu rajista, a inda jam'iyyar AD, APP da PDP suka samu nasarar takarar kujerar Majalisu, Gwamnoni da na Shugaban kasa. Jama'a da dama a wancan lokaci sun yi korafin cewa, faruwar wadannan lamurrori masu muhimmanci a siyasa cikin wata tara abu ne da ba zai haifar da da mai ido ba. Amma saboda zakwadi da kosawa da jama'a suka yi da mulkin kama-karya na Sani Abacha, sai aka daure duk da an san cewa akwai matsala.

Wannan mukalar ba tana nufin kawo maku tarihin abin da ya faru bane, amma tana son ta nuna maku dalilan da ya sa jama'a da yawa suka yi ruwa da tsaki don ganin Shugaba mai ci yanzu, Cif Olusegun Obasanjo ya dare kan gadon mulki a shekarar 1999. Ni da sauran 'yan jam'iyyarmu ta PDP muna sane da irin mummunar murdiyar da aka yi a babban taron da ya gudana a Jos, jama'a da dama na sane da irin kudaden da ya kewaya a tsakanin Delegates (Wakilai). Muna kuma sane da cewa akwai nakasu a cancantarsa, amma Shugabanninmu na Arewa suka yi kane-kane don ganin an zabe shi har suka nada masa suna Uba Sirajo.

A daidai wannan lokacin ne 'yan kabilarsa, Yarbawa, suka yi fatali da shi, mu ko muka rungume shi, muna ganin watakila shi ne mai ceton da ake ta sauraro zai zo ya ceci kasar nan daga halin ni'yasun da mulkin sojoji ya aukar na tsawon shekaru 15. Muna gama murnar cin zaben Obasanjo, ya fito da irin halayyarsa a fili, a inda ya nuna cewa shi ba dan goyo bane, tukwicin farko da ya yi mana shi ne rushe Hukumar tara rarar mai ta PTF, wanda ko makaho ya san cewa ta yi kokarin inganta rayuwar 'yan Nijeriya. Daga nan zuwa shekaru 50, alamomi da ire-iren ayyukan da ta gudanar ba zai bace ba.

Ba mu gama murmurewa daga wannan abu da ya yi mana ba, sai ya ba da sanawar dauke wasu Hukumomin Gwamnati masu muhimmanci daga Abuja zuwa Legas. Kan haka wasu 'yan majalisa sun kai kotu, amma ya yi watsi da hukuncin kotun. Ana cikin haka ya ba da sanarwar karin kudaden albarkatun man fetur. Dalilin cewa yin haka zai sa a rika samun fetur ba tare da wata wahala ba, kuma gwamnatinsa za ta samu kudaden yi ma jama'a aiki.

Mutane da dama na ta mamakin inda aka yi da rarar kudaden da aka samu, bayan soke PTF, da kuma kudaden da aka ce an kwato daga hannun iyalan Abacha, haka ma ana mamakin yadda irin makudan kudaden da aka samu sakamakon sayar da hannun jarin masana'antu da wasu hukumomin gwamnati suka shiga.

A zamaninsa ne kasar nan ta samu nasarar zama zakara a fagen cin hanci da rashawa, a inda kungiyar yaki da cin hanci da kuma karbar rashawa ta duniya ta sanar da cewa Nijeriya ce kasar da ta fi kowacce cin hanci da murde kudaden talakawa. Da farko mun nemi mu kaddamar, amma sai muka yi shiru bayan rahoton da mai binciken kudi na tarayya ya bayar na irin almundahanar da ake a gwamnatin shi Obasanjo, musamman a cikin fadar Shugaban kasa. Ashe dai surutun yaki da rashawar da gwamnatin ke yi tatsuniyar gizo da koki ce kawai. In ba haka ba me ya sa bai ba da izinin bincike da hukunta jami'an da rahoton Odita-Janar din ya zarga ba, amma kawai sai muka ga an yi masa ritaya?

A tarihin siyasar kasar nan, rikici bai taba munana ba tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa kamar yadda yake faruwa a zamaninsa. Irin katsalandar da ka yi ta yi a harkokin majalisa da yadda ya yi ta haifar da rudami da kokarin da bangaren gwamnatinsa ta yi dangane da bayanin shugabannin majalisa irin su Chuba Okadigbo da Ghali Na'abba, lamari ne mai ban takaici. A wannan karon ma hannunsa na nan dumu-dumu kan yadda aka yi zaben shugabannin majalisun na yanzu, abin da ya sa ake ganin cewa za su zame 'yan amshin Shata ne kawai. Kiyasi ya nuna da cewa mutanen da suka rasa rayukansu saboda rikice-rikicen addini, kabilanci da na siyasa a zangonsa na farko sun ninka wadanda yakin basasa ya lankwame a shekarar 1967-1970. Abin da ya fi tayar da hankali ma shi ne irin ko-in-kula da yake nunawa kan wasu rikice-rikicen. Misali, lokacin da 'yan kungiyar OPC suka dira kan Hausawa a Legas, suka karkashe su, suka kuma kona dukiyoyinsu, maimakon ya ba da umurnin hukunta shugabannin kungiyar, sai kawai aka sake su. Muna kuma sane da cewa da kansa ya ba da umurnin sojoji su auka wa mutanen Odi da na Zakibiam. Rikicin addini irin na garin Kaduna, Jos, Bauchi da Gombe sun lamushe rayukan mutane da dama, amma har yanzu ba mu ga wanda gwamnatinsa ta hukunta ba. Maimakon ya tsaya cikin kasar ma sai kawai tafiye-tafiyensa yake yi zuwa kasashen duniya.

Duk wadannan katobarar da ya yi ta tafkawa cikin shekaru hudu na farko da muka zabe shi, an kara dankara mana shi ta hanyar murde zaben fitar da gwani da aka gudanar a Abuja. Kowa ya san Dattijo Alex Ekweme muka zaba, amma ya yi amfani da mulki ya danne. Ni da sauran 'yan PDP mun san irin kamfen din sharri da muka yi ta yi kan dan takarar jam'iyyar ANPP, Janar Buhari, da yadda aka yi amfani da addini, kudi da danniya wajen ganin bai kai labari ba.

Maganar murdiya kuwa hatta Hukumar kasashen Turai da ta zo sa ido kan yadda aka gudanar da zaben ta yi bayanin cewa an tafka kazamin magudi. Abin da mu kanmu 'yan PDP ya ba mu kunya. Maganar zaben dai har yanzu yana kotu. To irin yadda ya sake taku a wannan karon mulkinsa na karshe ya fara ba mu tsoro. Abin da ya sa muke ganin cewa lallai za mu ci kwakwa. Eh! mana, to ga shi ko wata hudu bai yi kan karagar mulki ba, amma ya fara fito da tsare-tsaren da zai gallaza wa talaka. Karin kudin man fetur daga 26 zuwa 40 abu ne da bai nuna tausayi ba. Duk da cewa bayan yajin aikin gama-gari da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi an dawo da kudin zuwa 34. Irin yadda harkokin sufuri da na al'amuran yau da kullum suka tashi abu ne mai ban tsoro. Abin takaici shi ne irin halin ko-in-kula da yake nunawa. Ana cikin wannan hali ne ya tsallaka zuwa kasar Laberiya gayyatar dan ta'adda Charles Tailor, wanda kotun duniya mai shari'ar laifukan yaki ke nema ruwa a jallo saboda cin mutuncin bil-Adama da ya yi a zamanin mulkinsa, don ba shi mafakar siyasa. Wannan ma masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin cewa kuskure ne babba a fagen huldar difulomasiyya. Kokarin da yake neman yi na kai wa da komowa don fatattakar 'yan juyin mulki, shi ma wani abu ne da ake ganin lallai zai yi danasanin yin sa.

Masu iya magana na cewa ruwa ba ya tsami banza, kuma in bera na da sata, to lallai daddawa ma na da dan karen wari. Abin nufi a nan duk irin cin kashin da gwamnatin Obasanjo ke yi mana ai baan laifin na kanmu, musamman mu 'yan jam'iyyar PDP da muka tabbatar da ganin ya dawo, don ai da mu aka yi amfani wajen dukkan murdiyar da aka gudanar a wurare daban-daban cikin kasar nan. Haka ma sauran mutane na da nasu laifin don in da yau duk za mu fito kan titi mu ce ba ma so, to karkari a kashe dubu dari biyar cikinmu, amma ba abin da dan Nijeriya yake gudu sai mutuwa. Amma abin mamaki shi ne kullum mutuwar ake yi. Banda haka ma ai da mu ake amfani wajen far wa sauran jama'a, misali sojojin da 'yan sanda. Ina mai tabbatar maka da cewa gungun wadanda suka fi shan wahala a tsare-tsaren Gwamnatin nan sune 'yan sanda da sojoji. Banda rashin cikakken albashi a kan kari, ka ga barikokinsu sun zama kamar gidajen aladu. In kuma sun yi ritaya, a cikin irin wannan hali ne akan amfani da su don gallaza wa sauran jama'a. Misalin irin kashe jama'a da 'yan sanda suka yi lokacin yajin aikin kwanan baya Abuja da Legas ya isa.

To ba za mu yi tuya mu manta albasa ba, tun da an ce; 'ba a mugun sarki sai mugun bafade.' Abin da nake son nunawa shi ne ai ba Shugaba Obasanjo kadai yake tafiyar da mulkin kasar nan ba, yana da mataimaki da masu ba da shawara na musamman. Kuma ina da yakinin cewa da saninsu ko ma da shawarwarinsu wajen tsare-tsaren wannan gwamnati, saboda ai wasu manufofin sai an tattauna su a taron Majalisar Zartarwa ta Kasa, majalisar da duk Ministoci, masu ba da shawara na musamman da Mataimakin Shugaban kasa ke ciki. A kan haka ne jama'a ke nuna irin rashin jin dadinsu kan irin mutanen da aka nada Ministoci kwanan nan. Ana ganin cewa yawancinsu mutane ne masu dauke da guntun kashi. Wasu ma da kyar suka haye tacewar da majalisar dokoki ta yi masu saboda ire-iren abubuwan da suka tafka a harkokinsu na baya. Tabbas, irin wadannan mutane ba za su samu nacewa ba sosai kan tunkarar Shugaban kasa kan wasu lamurra. Tabbas wadannan shekaru hudu da ke gabanmu na mulkin Obasanjo, za su zama shekaru na ha'ula'i. Fatar mutane shi ne Allah Ya ba mu dauriya da karfin ran fuskantar tsare-tsarensa. Ga shi kuma Obasanjo da na kusa da shi, ina masu addu'ar Allah Ya jagorance su wajen tafiyar da lamurran kasar nan. Allah kuma Ya sa musu tausayin talakawa, Allah kuma Ya sa kada su manta da sashin ilmi, harkar noma, jin dadin ma'aikata, jin dadin 'yan fansho da tsaron lafiyar jama'a. Titunan kasar nan, 'yan fashi da makami da sauransu, Allah Ya ba su ikon gyara lamurran. Ni ko da ire-irena, muna fatar Allah Ya kare mulkin dimokradiyya. Allah Ya kuma kare Nijeriya. Amma ku sani PDP ta bar sake samu kuri'armu a zabe na gaba.

Komawa babban shafinmu                                   Komawa saman wannan shafin