Jaridar bunkasa kasuwanci da siyasa

Dangane da jaridar dillaliya

Ka tuntubi jaridar Dillaliya

Karanta jaridar Dillaliya a taskarta

Ka sayi jaridar Dillaliya

Ka duba wasikunku

Inganta sana'armu ce ta daukaka mu.

Manajan Mai Dabino

Daga Salisu Tukur

Manajan kamfanin Mai Dabino Yoghurt, Alhaji Ibrahim Lawal, ya ce gaskiya, rikon amana da inganta sana'arsu ya sa aka san Mai Dabino yoghurt ake kuma shan sa nesa da kusa.

Manajan ya shaida wa DILLALIYA cewa an fara sarrafa yoghurt din Mai Dabino ne a 19 ga watan Satumban 1997 da ma'aikata goma sha biyu kacal kuma a garin Katsina kadai, amma zuwa yanzu suna da ma'aikata 70 da kuma rassa a garuruwan Lagos, Kano, Zaria, Suleja da Funtua. Suna kuma da niyyar bude wasu sabbi a wasu garuruwan nan gaba kadan.

Manajan ya kuma shaida wa DILLALIYA cewa shi a tunaninsa ya kamata a ce zuwa yanzu sun kai kowace shiyya ta kasar nan, amma sai wasu matsaloli kamar na rashin tsai da wutar NEPA da ruwan famfo suka zama kafar ungulu ga wannan aniya tasu.

"Domin in babu tsayayyar wuta da ruwa dole ne ka yi tunanin samun mafita. Mafitar kuwa ita ce sayen babban janareto da samar da tsaftataccen ruwan famfo; wadannan abubuwan kuwa dole ne su lankwame daruruwan dubunnai, wadanda za a iya juya su ta hanyar kara yawan rassa," in ji shi.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da ta sama wa 'yan Nijeriya tsayayyar wuta da ruwa domin bunkasar kananan masana'antu da sauran sana'o'i wadanda za su rage mata nauyin rashin aikin yi da matasa ke fama da shi.

Da DILLALIYA ta tambaye shi kayayyakin da kamfanin Mai Dabino ke samarwa, sai ya ce zuwa yanzu dai suna samar da Yoghurt ne wanda Hukumar kula da lafiyar kayan abinci da magunguna, wato NAFDAC ta amince da shi, ta kuma ba su lamba tare da izinin sarrafa shi. Sannan suna yin tsaftataccen ruwan sha, suna kuma da niyyar fara lemo (Juice) da sauran wasu abubuwan taba-ka-lashe nan ba da dadewa ba.

Ya kuma shaida wa DILLALIYA cewa sirrin karbuwar kayansu shi ne gaskiyarsu ga abokansu, injuna na zamani da kuma dadin dandanon yoghurt dinsu gami da araharsu.


Komawa shafin farko